Hotunan yadda gobara ta lashe majami’ar Notre-Dame a Paris

Wata gagarumar gobara ta lashe ginin majami’ar Notre-Dame mai cike da kayan tarihi har husumiyar ginin ta rushe gaba daya.

Ma’aikatan kashe gobara sun yi wa tsohon ginin majami’ar da aka gina shi a karni na 12, wanda yayi suna saboda tsarin ginin da gwanayen magina suka tsara.

Dubban mazauna birnin Paris har ma da masu yawon bude idanu ne suka taru a kusa da ginin suna kallon yadda gobarar ke kara habaka.

@www.bbc.com/hausa

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *