Sani 313 Ne Halastaccen Sanatan Da Zai Wakilce Mu A Neja Ta Tsakiya – Yanga

An nemi magoya bayan Alhaji Sani Musa 313, zababben sanata wanda zai wakilci yankin Neja ta Tsakiya daga jam’iyyar APC da kar su yi kasa a guiwa akan hukunce-hukuncen da kotunan sauraren kararrakin zabe ke gabatarwa, domin ko jam’iyyar PDP da muke zargi da karyawa ko ba gaba ba tai irin wannan abinda ke tafiya ba yanzu. Bayanin hakan ya fito daga bakin kodinetan Sanatan a karamar hukumar Chanchanga kuma shugaban kidonetocin kananan hukumomi tara na yankin Neja ta tsakiya, Alhaji Hamza Yanga Buba.

Kodinetan ya cigaba da cewar muna da hujjojin da ke kara karfafa mana guiwa, mun tsaya takarar fidda gwani mun samu kuri’u sama da dubu talatin da tara yayin da abokin hamayyar mu ya tashi da kuri’u dubu biyar da doriya, kan haka hukumar zabe ta amince mana da nasararmu, bayan Sanata Dabid Umaru ya tafi kotun sauraren karar zabe mun gabatar da hujjojin mu kuma mun samu nasara akan shi, yau kuma muna jin rade-radin babban kotun daukaka kara wai ta baiwa Sanata Dabid Umaru, jama’a ina kira da babban murya da kowa ya kara hakuri, idan ma abinda ake yadawa gaskiya ne zamu daukaka kara, wadannan abubuwan da ake yi mana ana yin su ne dan a kawo hatsaniya a tsakanin mu, dan haka duk wanda ke kaunar Alhaji Sani Musa 313 kuma ya tabbatar da yin wannan gwagwarmayar da gaskiya kar ya karaya, Sanatan nan da muka zaba shi zai wakilce majalisar dattijai da yardar Allah.

Saboda haka masu maganar Automatic ticket ga sanata Dabid Umaru ina yake a dokokin Najeriya ko kuma a dokokin ita APC din, akwai wani Automatic ne bayan zaben fidda gwani, mun tafi kotu mu da muka ci zaben fidda gwani kotu ta tabbatar mana cewar mune ‘yan takara na gaskiya, duk abubuwan da ake bijirowa da su yanzu ba sa kan ka’idar siyasa kuma ina tabbatar wa magoya bayan mu cewar Alhaji Sani Musa 313 shi ne halastaccen Sanatan da zai wakilci zone ‘ B’ da ba za a yi mana fashin zaben mu ba da rana tsaka, zamu tafi supreme court bin kadin mu.

Dokar Najeriya ba wasan yara ba ne, kani da wa ne ke rigima amma ina da tabbacin gaskiya zai halinta, domin Najeriya ba family affairs ba ne. Duk kodinetocin mu ina jawo hankalinsu da cewar duk wanda ya takale su da maganar siyasa da cewar kar su mayar da hankali akan shi, na yi Imani da Allah cewar wannan kujerar ta Sani Musa 313 ne, don haka wanda ke tunanin yin wasa da dokokin Najeriya ya daina wahalar da kan shi, kowani dan siyasa da ke neman yin karko a siyasa ya rungumi jama’a, ya kuma tabbatar ya hada kan shi da talakawa da hakan ne kawai zai iya samun tagomashi da cigaban siyasarsa.

Alhaji Hamza Yanga Buba ya jawo hankalin shugabannin jam’iyyar APC ta jiha da kasa da su daina barin ana yiwa jam’iyya zagon kasa da sunan siyasa, domin idan mun samu nasara wannan itace karo na biyu da rike madafun ikon kasar nan amma abubuwan da ake yi a da sunan APC ba abinda yi mata na cigaba illa zubar kimarta a idon talaka, ya kamata mu dauki darasi daga abubuwan da suka faru ga PDP, domin Hausawa na cewa idan ka ga gemun dan uwanka ya kama da wuta to lallai ka shafa wa ta ka ruwa.

HAUSA LEADERSHIP

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *