Me ya sa fyade ke karuwar a Nijar?

News

Matsalar fyade na daga cikin abin da ke ciwa mutane tuwo a kwarya, inda lamarin ya zama tamkar ruwan dare.

Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun ce cikin shekaru biyu da suka gabata, an samu karuwar yi wa yara kanana fyade kusan sau hudu idan aka kwatanta da shekarun baya.

Ana danganta yawaitar ta’adar ga matasa da shaye-shayen muggan kwayoyi, da tabar wiwi da sauran kayan maye da ke dauke hankalin matasan su aikata fyaden ba tare da sanin abin da suke aikatawa ba.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun bayyana cewa rashin daukar mataki, da hukunta wadanda ake samu da aikata ta’adar da kuma kin kai kara gaban hukuma da wasu iyaye ke yi na daga cikin dalilan da ke janyo nakasu a kokarin da hukumomi ke yi na magance matsalar.

Malama Buzuwa ta wata kungiyar kare hakkin yara, ta shaidawa wakiliyar BBC cewa da iyaye za su daina shiru da bakinsu, a kuma daina rufawa wadanda suka aikata fyade asiri ko da kuwa dan uwa ne ya aikata da matsalar ta yi sauki.

Ba dai Nijar ce kadai kasar da ke fama da matsalar yi wa yara kananan fyade ba, ko a makofciyarta niajeriya lamarin ya kazance a dan tsakanin inda nan ma ake alakantawa da shaye-shaye da rashin tarbiyya da sauransu.

@/www.bbc.com/hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *