‘Yan bindiga sun ‘tayar da gari’ a Zamfara

News

Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa wasu ‘yan bindiga sun abka wani kauye inda suka kashe mutane da dama a karamar hukumar Shinkafi.

An kai harin ne a kauyen Kware a tsakiyar dare a ranar Lahadi, kuma baya ga kashe mutane ‘yan bindigar sun kone gidajen mutane da dama, kamar yadda wani mazauni kauyen wanda shi ma ya ce an kone gidansa ya tabbatarwa da BBC.

Ya ce sun kirga gawawwakin mutane kimanin 40 da ‘yan bindigar suka kashe.

Ya kuma ce sun gudu zuwa daji, yayin da mutanen kauyen da dama suka yi gudun hijira zuwa makwabta.

“Zuwa yanzu za mu iya cewa sun kwace ikon garin,” in ji shi.

Sai dai zuwa yanzu rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara ba ta fitar da sanarwa ba game da al’amarin.

Wannan harin na zuwa ne bayan ‘yan bindiga sun kashe mutane da dama a wani hari da suka kai yankin a ranar Alhamis.

@www.bbc.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *