Yadda likita ta koma mai daukar hoto a Abuja

News

Fatima Muhammad, mai shekara 23, ‘yar asalin jihar Katsina, ta yi karatun liktanci ne a jami’ar karatun likitanci (China Medical University) da ke lardin Liaoning a kasar China.

Sai dai yanzu tana wani asibiti a Abuja, inda take samun horon sanin makamar aikin likitanci.

A wata tattaunawa da ta yi da BBC ta bayyana mana yadda ta fara sana’ar daukar hoto da yadda take ji a matsayinta na ‘ya mace idan taje daukar hoto.

“Na fara daukar hoto a shekarar 2014, yanzu shekara ta biyar ke nan ina wannan sana’a,” in ji ta.

“Akwai hotunana da suka karade kafafen sada zumunta, wato sun zama Viral ke nan a harshen Inglishi.”

Har ila yau Fatima ta ce wasu hotunan da ta dauka mutane sun yi tayin sayensu.

Hoton babban masallacin Abuja shi ne hotonta wanda ya fi kowanne bazuwa.

Ya karade kafafen sada zumunta sosai a kwanakin baya.

Ta yi amfani da kyamara mai tashi sama wato Drone Camera inda ta dauki hoton.

Da aka tambaye ta likitanci za ta zaba ko daukar doto, sai ta ce mana:

Ta bayyana cewa tana son ta hada duka biyun ne a tare. “Domin duka abubuwa ne da ta ke kauna.”

Fatima ta ce tana fatan za ta zama wata tauraruwa da hotunan ta za su game duniya.”

Ta yi kira ga matasa mazansu da matansu da su yi aiki tukuru a kan abubuwan da suka sa a gaba.

Idan suka yi haka za su cimma “nasara a kan abubuwan da suka sa a gaba,” in ji ta.

@bbc.com/hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *