Yadda Amurka ke fuskantar matsanancin sanyi

News

Amurka na fuskantar matsanancin sanyi wanda aka shafe gomman shekaru ba a taba samun irinsa ba.

Ban da tsananin sanyi, akwai wata iska mai karfi daga yankin Arctic na arewacin duniya da ka iya kawo matsanancin sanyi na kasa da ma’aunin Celsius -53.

Jami’ai a jihar Iowa na gargadin mutane da su guji shakar numfashi mai yawa, kuma su rage yin magana idan sun fita wajen gidajensu.

Akalla mutum miliyan 55 ne ake sa ran yanayin matsanancin sanyi zai shafe su.

An ayyana dokar ta baci a jihohin tsakiyar Amurka Wisconsin da Michigan da IllinoisHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionAn ayyana dokar ta baci a jihohin Wisconsin da Michigan da Illinois

An ayyana dokar ta baci a jihohin tsakiyar Amurka kamar Wisconsin da Michigan da Illinois, har ma da jihohin da ke kudancin kasar kamar Alabama da Mississippi.

John Gagan, wani jami’in hukumar da ke kula yanayi na Amurka ya ce irin wannan tsananin sanyin na zuwa ne sau daya a gomman shekaru.

Ana kuma hasashen sanyin zai cigaba da karuwa har ranar Alhamis, jami’ai sun ce sanyi a birnin Chicago zai zarce na yankin Antarctica.

An dai soke fiye da sauka da tashin jiragen sama 1,100 daga ciki da wajen Amurka tun jiya Talata.

Motorists have been told to pack extra supplies and to take extra care when travellingHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionAn umarci masu mota su kiyaye a lokacin wannan matsanancin sanyin

Lamarin ya kai har hukumomi a yankin tsakiyar Amurka an rufe dubban makarantu da shaguna har ma da ofisoshin gwamnati.

Sannan hukumomin sun samar wa mutanen da ba su da wurin zuwa wuraren da za su fake daga wannan matsanancin sanyin a biranen Amurka da dama har da jihar Milwaukee.

@bbc.com/hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *