Kotu ta yi watsi da karar Walter Onnoghen

News

Kotun daukaka kara ta Najeriya ta yi watsi da bukatar da dakataccen alkalin alkalan kasar Walter Onnoghen ya gabatar ta neman kotun da’ar ma’aikan kasar ta dakatar da shari’arsa wadda gwamnatin Najeriya ta shigar.

A hukuncin da ta yanke ranar Laraba, kotun ta yi watsi da bukatar ce domin ba a gabatar da dalilan sauraron karar ba kamar yadda dokokin shari’a suka tanada.

Hukuncin na nufin alkalin alkalan zai ci gaba da fuskantar tuhuma a gaban kotun da’ar ma’aikatan, wadda ta dage zamanta domin dakon sakamakon karar da Mr Onnoghen ya daukaka.

Shugaba Buhari ya dakatar da Mista Onnoghen ne bisa shawarar kotun da’ar ma’aikata wacce ta samu alkalin alkalan da laifin kin bayyana cikakkun kaddarorinsa lokacin da aka nada shi kan mukamin a 2017.

Sai dai Mista Onnoghen ya ce ba da gangan ya yi hakan ba, yana mai cewa mantawa ya yi.

Hakan dai na zuwa ne kwana daya bayan majalisar shari’a ta kasar ta bai wa alkalin alkalan da aka dakatar da sabon mukaddashin da aka rantsar Mohammed Tanko Ibrahim wa’adin mako guda da su mayar da martani kan korafe-korafen da aka shigar gabanta.

Kungiyar lauyoyin kasar dai ta yi zanga-zanga kan matakin da Shugaba Buhari ya dauka kan Mista Onnoghen inda ta bukaci mambobinta da su kauracewa kotu tsawon kwana biyu daga ranar Litinin.

Sai dai wasu daga cikin ‘yan kungiyar sun ce ba za su fasa zuwa kotu ba.

Ita ma majalisar dattawan kasar ta shigar da kara a kotun kolin kasar inda ta bukace ta yanke hukunci kan ko ya dace Shugaba Buhari ya dakatar da alkalin alkalan Walter Onnoghen.

Sai dai wata sanarwa da shugaban masu rinjaye na majalisar, Ahmed Lawan, ya fitar ranar Litinin da ta barranta ‘yan jam’iyyar APC na majalisar daga kai shugaban kasar kotu, tana mai cewa shugabannin majalisar basu tuntube su ba kafin su kai Shugaba Buhari kotun.

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP da kasashen Amurka da Birtaniya da kuma tarayyar turai sun yi allawadai da dakatar da Mista Onnoghen.

Sai dai gwamnatin ta ce ba za ta amince da katsalandan daga kasashen waje cikin harkokin gidanta ba.

@bbc.com/hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *