Manufofin Atiku Suna Da Hadari Ga Nijeriya – Shehu Sani

Politics

Shehu Sani sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya bayyana shakku akan manufofin dan takarar PDP Alh. Atiku Abubakar.

Karanta: Tsaro: Rashin Ilimin Shugabanci Ne Babbar Matsalar ‘Yan Sanda – IG Adamu

In bamu mantaba kwanan nan ne Atiku ya tabbatar da aniyarsa ta sayarda Ma’aikatar NNPC da zarar aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, inda yace kashi goma cikin dari 10% kacal zai barwa gwamnati.

Yafadi hakan ne ga jaridar The African Reports Mai fita wata-wata. Atikun yaci gaba da cewa ta haka ne zai samo kudade don gina hanyoyi, asibitoci da ma’aikatun da zasu kawo cigaba a Nigeria.

Karanta: Buhari Ya Fallasa Wadanda Ke Daukar Nauyin Boko Haram

A martanin da Shehu Sani ya bayar akan wannan magana ta Atiku, sai yace wannan manufa tana da hadari kuma bazata haifar da da Mai ido ba. Ganin yadda ya fito yai ikirari a matsayin alkawarin aikin da zaiyi in aka zabeshi to tabbas da gaske yake zai yi wannan aika-aika.

Karanta: Rashawa: Atiku Ya Nemi A Binciki Surukin Shugaba Muhammadu Buhari.

Akarshe Sanatan ya buga misali da sayar da ma’aikatu irin su (NEPA) da makaman tanta, sayarwar bata Kawo wani alheri ga kasa ba sai ma kara lalata Al’amura da hakan yayi.

Gulmawuya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *