David de Gea kwararren gola ne – Ole Gunnar Solskjaer

David de GeaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionDe Gea ya koma United ne daga Atletico Madrid a shekarar 2011

David de Gea zai iya zama golan da ya fi kowanne kwarewa a kungiyar Manchester United, kamar yadda kocin riko na kungiyar Ole Gunnar Solskjaer ya bayyana.

Golan wanda dan kasar Spain ne ya cire kwallaye 11 a wasan da kungiyarsa ta doke Tottenham da ci 1-0 a filin wasa na Wembley ranar Lahadi.

Lokacin da ya kwashe shekara 11 a matsayin dan wasan gaban United, Solskjaer ya yi wasa da Edwin van der Sar da kuma Peter Schmeichel.

“Na san manyan gololi a wannan kungiya kuma ina tunanin De Gea yana kalubalantar Edwin da kuma Peter wajen kafa tarihi,” in ji Solskjaer.

Kwallaye 11 da De Gea ya cire su ne mafi yawa a gasar firimiya yayin da ya taimaka wa kungiyar ta samu nasara a wasanni shida a jere a karkashin jagorancin Solskjaer.

De Gea ya koma United ne daga Atletico Madrid a shekarar 2011 kuma ya samu kyautar kwarzon dan kwallon kungiyar sau hudu.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *