Bai kamata a sake zaben Buhari ba – Dattawan Arewa

News
Farfesa Abdullahi Ango shugaban kungiyar dattawan arewa

Latsa alamar lasifika a kan hoton sama domin sauraren rahoton Nura Ringim

Kungiyar dattawan arewacin Najeriya da ake kira Northern Elders Forum ta sanar da janye goyon bayanta ga sake zaben shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban kungiyar Farfesa Ango Abdullahi ya shaida wa BBC cewa sun yanke wannan shawarar ne saboda abin da ya kira “ba wani abin ci gaba da Buhari ya yi wa arewa a kusan shekaru hudu na mulkinsa.”

“Buhari ya gaza wajen magance talauci da matsalar ilimi a arewacn Najeriya,” in ji Farfesa Ango.

Ya ce arewacin Najeriya ne dandalin talauci, kuma yankin ne ya dage wajen ganin Buhari ya lashe zaben shugaban kasa a 2015.

Amma Injiniya Khailani Muhammad shugaban ‘yan a kasa a tsare na kasa na shugaba Buhari, ya yi watsi da ikirarin na Farfesa Ango.

Ya ce su Farfesa Ango sun yi hakan ne don kansu ba da yawun mutanen arewa ba, “Sai don abin da Atiku zai dauka ya ba su.”

Ya kuma ce Buhari yana iya kokarinsa, domin ba lokaci daya ake yin gyara ba sai an dauki lokaci.

  • Ba mu hade wa Buhari kai ba – IBB
  • Wane tasiri hadewar APC da UPP ke da shi a zaben 2019?

A cikin bayanin da Farfesa Ango ya yi ya ce “ba mu yaba da ayyukan da shugaban kasa da gwamnonin arewa suka yi ba na gwamanatin APC.”

“Mun sa ran za a samu canji bayan Buhari ya ci zabe amma mun zuba ido ba mu ga komi ba.”

“Idan ba wani abu ya canza ba, bai kamata a goyi bayan shi idan ya sake neman zabe ba.”

Farfesan ya kara da cewa “idan ma Buhari bai ci ba, wani dan arewa ne zai ci zaben.”

Ya ce sun dade da yanke shawarar juya wa Buhari baya tun watanni da dama da suka gabata kafin yanzu.

“Saboda haka ya kamata a ba su notis, za mu fadakar da mutanen arewa cewa sun gaza saboda haka idan lokaci ya dawo suna neman kuri’a a ki zabensu.”

Amma a martaninsa, Injiniya Khailani ya ce ” Idan su da ke kiran kansu dattawa sun damu da matsalolin arewa me ya sa ba su tashi tsaye ba wajen an tayar da masaku da masana’antun da suka durkushe.”

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.