Yan Taliban sun sa ‘Messi’ ya tsere daga gidansu

Afghan boy Murtaza Ahmadi posing with a jersey sent to him by Argentine football star Lionel Messi in 2016Hakkin mallakar hotoAFP / UNICEF
Image captionMurtaza Ahmadi sanye da rigar da Messi ya aike masa

Yaron nan dan kasar Afghanistan wanda ya yi suna a shafukan intanet saboda kaunar da yake yi wa fitaccen dan kwallon kafa Lionel Messi ya tsere daga gidansu karo na biyu sakamakon barazanar ‘yan Taliban.

Daga bisani ne ya gana da Messi a Qatar.

Iyayensa sun ce yanzu sun tsere daga gidansu da ke Afghanistan bayan kungiyar ‘yan ta’adda ta Taliban ta yi musu barazana kan rayuwarsu.

Suna zaune ne a lardin Ghazni da ke kudu maso gabashin kasar – inda masu tayar da kayar baya ke hara – sannan suka tsere zuwa Kabul, babban birnin kasar.

Iyayensa sun taba neman mafaka ta wucin-gadi a Pakistan a 2016, amma sun koma kasarsu bayan kudinsu ya kare, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

Murtaza yana dan shekara biyar a duniya lokacin da ya sanya rigar ta jakar leda mai launin shudi da fari irin wacce ‘yan wasan kwallon kafar Argentina inda Messi yake wa kyaftin suke sanya wa.

Rigar na dauke da lamba 10 wacce Messi ke sanya wa.

Bidiyon Murtaza Ahmadi sanye da rigar jakar leda ta dan kwallon kafa Lionel Messi

Bayan hotonsa ya watsu a shafukan sada zumunta, mutane sun yi kira da a nemo shi domin ya gaba da Messi.

Lokacin da aka fitar da sunan yaron, dan kwallon kafar ya aike masa da sako – ciki har da rigarsa ta kwallon kafa wacce ya sanya wa hannu.

Daga bisani ne Messi ya gayyaci Murtaza zuwa Doha domin su gana lokacin da Barcelona ta buga wasan sada zumunta a Doha a 2016. Yaron da kuma Messi sun shiga filin wasa tare.

Sai dai iyayensa sun ce suna jin tsoro sunan da ya yi ne ya sa ‘yan Taliban suke yi musu barazana.

Murtaza Ahmadi, a young fan of Barcelona star Lionel Messi, plays with a friend in Kabul, Afghanistan, 03 December 2018Hakkin mallakar hotoEPA
Image captionMurtaza da iyayensa da kuma ‘yan uwansa hudu na zaune a gida mai daki daya a Kabul.
BBC Hausa 

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *