EFCC ta gurfanar da Dakingari a gaban kotu

DakingariHakkin mallakar hotoTWITTER

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, EFCC, ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kebbi da ke arewacin kasar, Usman Saidu Dakingari, a gaban kotu bisa zargin halasta kudin haramun.

Mai magana da yawun hukumar, Tony Orilade, ya ce sun gurfanar da Dakingari da wasu mutum biyu a kotu ne bisa zargin aikata laifuka 13, ciki har da hada baki wurin aikata laifi da halasta kudin haramun da suka kai N450m.

An gurfanar da mutanen uku ne a babbar kotun tarayya da ke Kebbi wacce mai shari’a Basse Onu ke jagoranta.

  • EFCC za ta gurfanar da Diezani a gaban kotu
  • Shaidu a shari’ar Murtala Nyako sun yi mutuwar al’ajabi

Sanarwar da EFCC ta fitar ranar Laraba ta ce ana zargin Dakingari da Sunday Dogonyaro da kuma Garba Rabiu Kamba da laifin karbar N450m wadanda wani kaso ne cikin $115m da tsohuwar ministar man fetur ta kasar Deizani Alison-Madueke ta raba wa ‘yan siyasa gabanin zaben 2015 da zummar sauya alakar zaben.

Sai dai mutanen sun ce basu aikata laifin ba.

Alkali Onu ya bukaci EFCC ta ci gaba da tsare mutanen sannan ya dage sauraren karar zuwa ranar goma ga wataan Disamba domin yin hukuncin kan yiwuwar bayar da belin su.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *