‘An ci zarafin mata fiye da 500 a wata 10 a Kano’

Taswirar wasu jihohin Najeriya

Wata lauya a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Barista Maryam Ahmed Sabo, ta shaida wa BBC cewa, matsalar cin zarafin mata da kananan yara musamman a Najeriya tana da girman gaske.

Ta ce ko wajen tafiya da ake yi da mata fatauci ko safararsu, a kan musgunawa wasu, ko yi musu fyade ko kuma wulakantasu.

Baristar ta ce, baya ga cin zarafi ta hanyar fyade, a kan ci zarafinsu ta hanyar yi musu kaciya ko kuma fadan cikin gida.

  • Najeriya: Mace ta ‘kashe’ mijinta da maganin bera a Kano
  • ‘Illolin da auren dole kan haifar’
  • Malamin Islamiyya ya yi wa yarinya ‘fyade’ a Kano

Maryam Ahmad Sabo ta ce, cin zarafin mata da kananan yara yafi kamari a jihohin Lagos da Kano da kuma jihar Borno, amma kuma duk da haka ba bu jihar da a Najeriya ba a samun wannan matsala ta cin zarafin mata.

Ta ce, yara tun daga jaririya ‘yar wata daya zuwa ‘yan shekara 14, sun fi fuskantar wannan matsala a Najeriya.

Barista Maryam ta ce ” A jihar Kano kadai, tsakanin farkon shekara 2018 zuwa watan Oktoban shekarar, an ci zarafin yara fiye da 500’.

Ta ce abubuwa da dama ne ke haddasa afkuwar irin wannan matsala, kamar sakaci na iyaye da na masu bayar da tarbiyya, akwai rashin jin tsoron Allah da kuma masu aikata haka saboda biyan wata bukata ta su ta daban.

Baristar ta ce, tallace-tallacen da ‘ya’ya mata ke yi ma na janyo aci zarafinsu ta hanyoyi daban-daban, haka auren dole ma na janyo cin zarafin ‘ya’ya mata ta hanyar doka.

Ta ce da za a rinka fitowa ana fada idan an samu matsalar cin zarafin yara kamar yi musu fyade, kuma a daina kyamatar irin wadanda wannan masifa ta afkawa, a hadu a dauki matakin da ya dace, to da lallai an samu raguwar samun wannan matsala musamman a Najeriya.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *