Buhari ‘yana son yin watsi da kudirin dokar zabe’

Gamayyar jam’iyyun siyasar Najeriya, CUPP, sun zargi shugaba Muhammadu Buhari da niyyar yin watsi da kudirin dokar zabe ta shekara ta 2018 da aka yi wa gyara.

Wani mai magana da yawun gamayyar, Ikenga Ugochinyere, ya yi zargin cewa shugaba Buhari mai yiwuwa ya yi amfani da wata hujja daga cikin dokokin kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta yamma, domin cimma burin kin sanya hannu a dokar zaben ta Najeriya da aka gyara.

A lokacin da yake wannan kalamai a wani taron manema labarai, Mista Ugochinyere ya ce sun farga da wasu bayanai sirri da ke tabbatar musu da cewa shugaban kasar ya na son ya hana ‘yan kasar samun dokar da ta dace wanda za ta kai su ga gudanar da zabe cikin ‘yanci da adalci.

Ya kara da cewa kudirin zaben da aka yi wa gyara na kunshe da abubuwa da dama da za su magance magudin zabe da kusan kashi 40 cikin 100 domin haka kin aiwatar da shi babbar barazana ce ga zaben kasar da ke tafe, kuma za su kalubalanci hakan a kotu.

Sai dai jam’iyyar APC mai mulkin kasar ta yi watsi da wadanan zarge-zarge da suka bayyana da aikin sojin baka ganin cewa lokacin zabe ya karato.

Jami’in walwala na jam’iyyar, Ibrahim Masari, ya shaida wa BBC cewa yanzu lokaci ne da ake hayar mutane domin yada farfaganda da kuma bata suna.

Masu sharhi kan lamuran siyasa dai a kasar na gani cewa rashin sanin takamaiman bayyani dangane da halin da ake ciki, a kan kudirin dokar zaben yayin da zaben ke karatowa wani yanayi ne dai zai ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a fadin kasar.

@/www.bbc.com/hausa

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *