Burundi za ta rufe ofishin kare hakkin dan adam na MDD

Gwamnatin Burundi ta umarci hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya da ta rufe ofishinta da ke kasar cikin wata biyu.

Kamfanin dillancin labarai na AFP da hukumar harkokin wajen kasar da kuma wasu majiyoyin Majalisar Dinkin Duniyar suka bayyana haka.

Wani wanda ba ya so a bayyana sunansa daga bangaren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa”gwamnatin Burundi tana kara tsanantawa a kullum ga kasashen duniya.”

Burundi dai ta kauracewa wani zama na kasashen gabashin Afirka a watan Nuwamba.

Zaman ya mayar da hankali ne kan rikice-rikicen siyasa da ke faruwa a kasar.

A shekara ta 2017, Burundi ta fice daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya wato ICC, saboda kaddamar da bincike da aka yi a kan kasar sakamakon zargin ta da manyan laifuka.

An dai fara tashin hankali a kasar ne tun bayan da Shugaba Pierre Nkurunziza ya bayyana aniyarsa ta kara tsayawa takara karo na uku.

Wannan tayar da zaune tsaye a kasar ya yi sakamakon mutuwar daruruwan mutane.

Sama da mutum dubu 400 suka yi hijira, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

@www.bbc.com/hausa

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *