Majalisa ba ta da hurumin bincikar Ganduje – Kotu

Wata babbar kotun jihar Kano a Najeriya ta haramta wa majalisar dokokin jihar gudanar da bincike a kan wani hoton bidiyo da ke nuna Gwamna Abdullahi Ganduje yana karbar wasu daloli da ake zargin cin hanci ne.

Wata kungiyar lauyoyi masu fafutukar kare demokuradiyya ne suka shigar da karar, inda suka kalubalanci majalisar cewa ba ta da hurumin gudanar da binciken.

Kotun wadda mai shari’a Ahmad Tijjani Badamasi ya jagoranci zaman nata ta amince da bukatun da bangaren mai karar ya gabatar mata, ciki har da haramta wa majalisar gudanar da bincike a kan Gwamna Ganduje, kasancewar yana da rigar kariya, kuma ba aikin majalisar ba ne gudanar da bincike a kan miyagun laifuka.

Kotun ta jaddada cewa ‘yan sanda da hukumomi dangin EFCC, wato mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati da ICPC, su ne kundin tsarin mulkin kasa ya dora musu alhakin gudanar da bincike a kan zargin da ake yi wa Gwamnan, don haka kamata ya yi a tura musu hotunan bidiyon tun lokacin da aka same su, don su yi aikinsu.

Barrister Mohammed Zubairu shi ne shugaban kungiyar lauyoyi masu rajin kare demokuradiyya a Najeriya, wanda ya shigar da karar a madadin kungiyar, kuma ya ce wannan nasara ba ta su ba ce ta demukradiya ce.

Wannan layi ne

“Mu ba damuwarmu ba ce a yi bincike kan gwamna ko a’a, so muke a bar kundin tsarin mulki ya yi aikinsa,” in ji shi.

Shi kuwa Barrister Mohammed Waziri lauyan da ya tsaya wa majalisar dokokin jihar Kano, cewa ya yi za su kai al’amarin ga majalisa domin yin nazari kan mataki na gaba, na daukaka kara ko a’a.

Ganduje bai amsa gayyatar majalisa ba a zaman da ta yi sai ya tura kwamishinan yada labaransa
Image captionGanduje bai amsa gayyatar majalisa ba a zaman da ta yi sai ya tura kwamishinan yada labaransa

Shugaban kwamitin majalisar dokokin da ke gudanar da bincike a kan Gwamnan, wato Hon Bappah Babba Dan Agundi, ya kuma shaida wa BBC cewa abu ne da ba shi kadai zai yanke hukunci ba sai sun yi zama na musamman a majalisa kan hakan.

Wannan hukuncin dai za a iya cewa babban cikas ne ga yunkurin majalisar dokokin na ikirarin da ta yi cewa za ta bi diddigi har sai ta gano gaskiyar lamarin.

Wani, danjarida, Ja’afar Ja’afar ne dai ya fara wallafa hotunan bidiyon a jaridarsa ta intanet, lamarin da ya ja hankalin majalisar dokokin jihar Kano ta fara gudanar da bincike a kan zargin da ake yi wa gwamnan.

Bayan wannan kotun ma, akwai wata shari’ar a gaban wata babbar kotun jihar Kanon, inda Gwamna Ganduje ya shigar da karar dan jarida Ja’afar Ja’afar, yana zarginsa da yi masa kazafi, kana ya nemi kotu hana shi ci gaba da yada hotunan bidiyon, tare da biyan gwamnan diyyar naira miliyon dubu uku ta bata masa suna.

@/www.bbc.com/hausa

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *