Jami’yyun siyasar Najeriya sun yi wa INEC raddi kan kudin zabe

News

Jam’iyyun siyasa a Najeriya sun bayyana mabambantan ra’ayi kan kalaman da hukumar zaben kasar, INEC, ta yi cewa za ta yi amfani da wasu hanyoyi domin bin diddigin kudaden da jam’iyyun siyasa ke kashewa, a lokacin yakin neman zabe.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta ce matakin ya ba ta mamaki.

Alhaji Yahaya Ability, wani jigo a jam’iyyar PDP a jihar Niger, ya yi kira ga INEC ta tabbatar ta yi adalci.

“Jam’iyyarmu ba ta da kudi, ba mu da gwamnati saboda haka nan gwargwadon abin da muke kasuwanci shi ne muka ga ya dace mu tattara mu zo mu tafi zabe,” in ji shi.

Ita kuwa jam’iyyar APC mai mulki ta ce matakin da hukumar zaben ta dauka ya yi daidai saboda, a cewarta, wannan shi ne zai bambance tsaki da tsakuwa.

Honourable Faruk Adamu Aliyu Birnin Kudu, jigo a jamiyyar APC mai mulki, ya ce matakin zai sa a gane wadanda suke kokarin kwatantawa da kuma wadanda suka rika almundahana da kudin mutane .

“Ina son na tabbatar da cewa a yanzu da nake magana babu wani naira daya da ta cikin jami’yyar APC wadda ba karbar aka yi daga hannun yan jami’yya ba. Misali, kwanan aka sayar da fom-fom na tsayawa takara wadanda mutane da yawa sun yi karaji a kai, don me ya sa ya yi tsada.”

Sai dai wasu masu sharhi a kan kasar sun nuna shaku a kan ko hukumar zaben za ta iya wannan aiki na sa ido kan makudaden kudaden da jam’iyyu suke kashewa a lokutan zabe, saboda a cewarsu baya ta sha korafin cewa ayyuka sun yi mata yawa.

@www.bbc.com/hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *