Sanchez zai yi jinya mai tsawo – Mourinho

Sports

Dan wasan Manchester United Alexis Sanchez zai yi jinya mai tsawo saboda raunin da ya samu a agara, kamar yadda kocin kungiyar Jose Mourinho ya bayyana.

Dan wasan mai shekara 29 ya ji rauni ne lokacin da yake atisaye a ranar Alhamis.

Sai dai har yanzu ba a dauki hoton raunin ba, amma Mourinho ya ce “yana fama da raunin”.

“Ba karamin rauni ba ne wanda zai iya warkewa a cikin mako guda ko kwana 10,” in ji Mourinho.

Mourinho ya ce raunin ya fi wanda Victor Lindelof ya ji muni.

Lindelof ya ji raunin ne lokacin da United take karawa da Crystal Palace a ranar Asabar, ana saran sai badi zai dawo taka leda.

Har ila yau, game da Sanchez, Mourinho ya ce: “Mummunan raunin da dan wasan ya ji. Ba a dauki hoton raunin ba tukunna.”

“Amma a fahimta ta ina ganin ba karamin rauni ne, zai kwashe lokaci mai tsawo yana jinya,” in ji shi.

@www.bbc.com/hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *