‘Sabuwar kungiyar masu wa’azi ta bulla a Sokoto’

News

Rahotanni a Najeriya sun ce wata sabuwar kungiya ta masu ikirarin wa’azin Musulunci dauke da miyagun makamai, ta bulla a cikin jihar Sakoto daga jamhuriyyar Nijar mai makwabtaka da kasar.

Watannin biyu da suka gabata ake zargin ‘ya’yan kungiyar sun soma bula a wasu garuruwa na yankin karamar hukumar Tangaza kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaidawa BBC.

Mutumin da ya bukaci a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce ‘ya’yan kungiyar na bin kauyuka suna “karbar zakka daga masu abin hannu,” kuma suna yin “bulala ga mutanen da suka aikata abubuwan assha da suka saba wa dokokin addinin Musulunci.”

Sai dai duk kokarinmu na neman ji daga bakin jami’an tsaro a jihar ya ci tura.

Ya kuma shaida cewa ‘yan kungiyar sun fi mutum 200, kuma cikinsu akwai fulani da turawa da larabawa dauke da rawani da bindigogi.

”Suna bin gida-gida don karba kudade, mai rago zai ba da naira 2000, mai kiwon sa kuma zai ba da naira 500.”

Mutumin ya kuma shaida cewa suna kai yara cikin daji, suna koya musu wasu abubuwa, “idan za su dawo da su, sai su basu babur.”

‘Bullar ‘Yan Hakika barazana ce ga tsaro’ a Najeriya
Boko Haram ‘na kai wa sojoji hari da jirage marasa matuka’
An bukaci jami’an tsaro su rage yin fara’a
Yankin Tangaza a jihar Sokoto na makwabtaka da jamhuriyar Nijar inda ake zargin ‘yan sabuwar kungiyar da shigo wa.

Wannan al’amari dai na haifar da barazanar tsaro a yankin, kuma zuwa yanzu jami’an tsaro ba su tabbatar da wannan labarin ba.

Ko a kwanakin baya sai da aka yada wani bayanin sirri da ke kunshe cikin wata wasika ta kafafafen sadarwa na intanet, a kan bullar wata kungiyar addini mai suna ‘yan Hakika a jihohin Adamawa da Nasarawa, abin da ya kai ga sojojin na ankarar da sauran jami’an tsaro game da kungiyar.

Malaman addini dai na cewa bayyana irin wadanan kungiyoyi na da hadari a kasa irin Najeriya, idan aka yi la’akari da halin da kasar ta tsinci kanta ta rikicin Boko Haram.

@www.bbc.com/hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *