An kirkiri shafin yaki da labaran karya a Najeriya

News

An kaddamar da wani sabon shafin mai suna ‘CrossCheck Nigeria’ a ci gaba da kokari da daukar matakan yaki da labaran karya, gabanin babban zaben kasar da ke tafe a watan Fabarairu.

Shafin zai bai wa ‘yan jarida da kafofin yada labarai na sassan kasar damar yin aiki tare domin bincike da watsi da jita-jita, musamman wadanda ake yada wa ta shafukan sada zumunta.

Shafin zai rika ankarar da al’umma da ba su bayanai da kuma damar wallafa hotuna da bidiyo da wasu bayanai ta manhajar WhatsApp ko kuma ta shafin na CrossCheck Nigeria a kan abubuwa da ake bukatar tantance sahihancinsu

Cikakken bincike zai bayyanan a shafin kadai idan abokan hulda kamar biyar suka amince da bayanan, a cewar kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, wanda ke cikin wadanda za su gudanar da wannan shiri.

Kusan ‘yan jarida 46 daga kafafen watsa labarai 15 sun halarci taron kwana biyu na horarwa da ake yi wa taken ”boot camp” a turance a Lagos wanda masu goyon baya da tallafa wa shirin suka shirya.

Shiri ne dai na hadin gwiwa tsakanin kungiyoyi masu zaman kansu da suka hada da First Draft News ta Burtaniya da Cibiyar binciken rahotanni ta duniya, ICIR, da kuma ma’aikatan Jaridar Nigeria Tribune.

Daraktan zartarwa a Cibiyar ICIR, Daya Aiyetan, wanda ke sa ido a kan shirin, ya ce Facebook da Twitter da WhatsApp sun kasance kafofin da ‘yan siyasa ke amfani da su wajen watsa labaran karya da farfaganda.

@www.bbc.com/hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *