Buhari ya rage kudin jarrabawar JAMB da NECO

News

Gwamnatin Najeriya ta amince a rage kudin fom din Joint Admission and Matriculation Board (JAMB) da National Examination Council (NECO).

Daga yanzu duk dalibin da zai rubuta jarrabawar kammala sakandare, NECO, zai sayi fom din ne a kan N9,850 maimakon N11,350 da aka saba saya.

Kazalika an rage kudin fom din jarrabawar makarantun gaba da sakandare daga N5,000 zuwa N3,500.

Mai taimaka wa shugaban kasar a kan shafukan sada zumunta na zamani, Malam Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

https://twitter.com/intent/like?tweet_id=1067778890804928512

Ya ce an dauki matakin ne bayan taron mako-mako na majalisar zartarwar kasar da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta ranar Laraba a fadar shugaban Najeriya da ke Abuja.

A cewarsa, wannan sabon tsari zai soma aiki ne daga watan Janairun 2019.

Ministan ilimin Najeriya, Malam Adamu Adamu, wanda ya yi wa manema labarai jawabi bayan kammala taron, ya ce shi ne ya gabatar da bukatar rage kudin fom din JAMB da NECO bayan ya sha samun korafe-korafe daga wurin iyayen dalibai kan tsadar fom din.

Hukumar da ke kula da jarrabawar JAMB ta ja hankalin ‘yan kasar tun lokacin da Ishaq Oloyede ya zama shugabanta inda take tara miliyoyin naira bisa fam-faman da take sayarwa domin samar da kudin shiga ga gwamnatin kasar.

Ko da a watan Mayun da ya gabata sai da majalisar wakilan Najeriya ta yi kira ga ma’aikatar ilimi ta tarayya da ta rage kudin fom din JAMB.

@www.bbc.com/hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *