An dakatar da sarakunan Zamfara daga aiki kan barayin shanu

Gwamnatin jihar Zamfara da ke Najeriya ta ce ta dakatar da wasu sarakuna daga mukamansu bisa zarginsu da alaka da ‘yan fashin shanu da masu garkuwa da mutane.

Kwamishinan kananan hukumomi da masarautun jihar, Alhaji Bello Dankande, ya shaida wa BBC cewa an dakatar da hakimai uku sannan na hudu ya gudu.

“Duk wani basaraken da ka ga mun dakatar, mun samu labari yana mu’amala da wadannan ‘yan ta’adda. Misali, akwai wani uban kasa da aka kawo mana korafi a kansa cewa, na daya, ya tura galadimansa ya karbi belin barayi daga hannun ‘yan sanda.

“Haka kuma ya karbi kudi daga hannun wani dan ta’adda. Mutanen garin sun zo sun ce ya karbi N50,000,” in ji kwamishinan.

Ya kara da cewa za a gudanar da bincike kan hakiman sannan a tube rawunan da ke kansu “kafin a gabatar da su a gaban shari’a.”

Matsalar satar mutane domin karbar kudin fansa da kuma ta barayin shanu ta yi kamari a jihar Zamfara, inda a wasu lokutan barayin suke kashe mutanen da suka sace.

A watan Mayun ma an lalata bindigogi karkashin wani shirin yin afuwa da gwamnati jihar ta bullo da shi a bara
Image captionA watan Mayun ma an lalata bindigogi karkashin wani shirin yin afuwa da gwamnati jihar ta bullo da shi a bara

Ko da a makon jiya sai da wasu rahotanni suka ce an bayar da kudin fansa kafin a sako wasu tagwaye ‘yan mata da aka sace a jihar.

Gwamnatin jihar ta sha cewa tana daukar mataki domin shawo kan matsalar, ko da yake ana zarginta da hannu a batun amma ta musanta zargin.

Wannan layi ne

Karin bayani game da Zamfara:

  • Kashi 67.5 ke rayuwa cikin talauci
  • Iya karatu da rubutu: Kashi 54.7
  • Take: Noma tushen arzikinmu
  • Yawancin mutanen jihar manoma ne daga Hausa Fulani
  • Yawan jama’a: Miliyan hudu da rabi (Alkalumman shekarar 2016)
  • Musulmi ne mafi yawa
  • Jihar da aka fara kaddamar da Shari’a – a 2000
  • Madogara: Shafin alkalumma na Najeriya da wasu

Sharhi kan tarihin rikice-rikice a Zamfara – Daga Kadariyya Ahmed

Gwamnatocin da suka mulki kasar a jejjere sun ta yin buris wajen kawo maslaha ta dindindin kan matsolin da ke addabar jihar Zamfara.

A yayin da matsalar barayin shanu ta zama bala’i ga jihar Zamfara, Gwamna Abdulaziz Yari ya samar da kungiyar ‘yan kato da gora don yakar maharan a shekarar 2013.

Sai dai ba a dauki dogon lokaci ba mazauna yankin suka fara korafi kan ‘yan kato da gorar, wadanda a yanzu su ma suke gallabar mutanen da ya kamata su kare da sace-sace.

Ana zargin cewa yaran Buharin Daji (mai rike da lasifika) ne, wanda aka kashe farkon watan Maris ke ci gaba da aikata fashi
Image captionAna zargin cewa yaran Buharin Daji (mai rike da lasifika) ne, wanda aka kashe farkon watan Maris ke ci gaba da aikata fashi

Hakan ta sa kauyukan da ke fama da matsalar barayin shanu da ‘yan kato da gora suka fara kokarin ganin sunkare kansu da duk abun da ya kamata.

Daga haka sai rikicin ya kara ruruwa ta hanyar kai hare-hare da daukar fansa. A haka sai a ka kasa cimma kokarin shirin yin afuwa da aka so gabatarwa.

A yanzu dai muna ganin yadda rikici ke kara bazuwa da karuwa kuma ga alama ba a san hanyoyin da za a bi a shawo kansa ba.

Abun da yake a bayyane kawai shi ne yadda dumbin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ke ci gaba da mutuwa.

@www.bbc.com/hausa

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *