An harbe fitaccen dan jarida a Idlib

News

An Harbe wani fitaccen dan jarida mai gabatar da shirin Radiyo a yankin Idlib da ke arewacin Syria.

‘Yan bindiga ne suka harbe dan jaridar mai fafutuka Raed Fares a arewa maso gabashin garin Kafranbel.

Ba wannan ne karon farko da ake kai wa ma’aikatan gidan Radiyon Fresh mai zaman kansa hari ba a Syria, wanda ya ke gabatar da shiri kai-tsaye daga tsakiyar yankin da ‘yan adawa ke iko da shi a Syria.

Mayakan kungiyar Nusra Front mai alaka da al-Qaeda sun sha yi wa Fares barazana ciki har da kama shi a shekarar 2016 daga bisani suka sake shi.

Ita ma kungiyar Hayat Tahrir al-sham ta bukaci gidan radiyon Fresh ya dakatar da gabatar da shirye-shirye amma duk da haka suka ci gaba da aikinsu wanda Fares shi ne fitaccen mai gabatarwa.

Makusantan dan jaridar sun shaidawa BBC cewa daman an sha yi ma sa barazana kusan sau uku a jere, sun kuma yi kiran ya bar yankin Idlib amma sai dai ya yi murmushi ba tare da daukar mataki ba.

Shi ma shugaban kungiyar Syrian Network Fadel Abdel Ghany, wanda aminin Mista Fares ne ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa mutuwar dan jaridar babban rashi ne.

@www.bbc.com/hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *