Yadda ake ‘binne layu’ a wata makabarta a Kano

News

Wasu masu kula da makabarta a jihar Kano sun tono wadansu layu da wadansu mutane ke binne wa a kaburbura a wata makabarta da ke jihar.

Wani wanda ya shafe shekara 13 yana aikin hakar kabari a makabartar Tukuntawa, Abu Gwadebe, ya shaida wa BBC yadda suke gano layun da ake binne wa a makabartar.

“Yawancin layun da abubuwan da ake binne wa a kaburburan suna dauke da wani turare wanda kunama da sauran kwari suke son kamshinsa. Saboda da haka idan muka zo da safe mu ka ga kwari ko kuda na kewaye wani wuri, to sai mu tono wurin.” in ji Abu.

Uba Ibrahim shi ma ya shafe shekara 11 yana aiki a makabartar, amma shi kira ya yi ga gwamnatin da ta samar da fitilun lantarki da za su taimaka wajen rage aikata miyagun ayyuka a makabartar.

Wasu na danganta irin wadannan binne-binne a makabartu da tsafe-tsafe domin cimma wasu bukatu.

A kan samu karuwar irin wadannan al’adu ne lokacin da zabuka suka kawo jiki.

@www.bbc.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *