An Zarge Ni Da Cewar Ni Na Haddasa Boko Haram Domin Rage Al’ummar Arewa Saboda Na Ci Zaben 2015, Cewar Jonathan

 

Tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya ce an zarge shi da cewa shi ya kawo Boko Haram don rage al’ummar arewa da hakan zai ba shi damar tazarce a 2015 da ya ce ya zama mai muhimmanci ya yi bayani don a fahimci gaskiyar lamarin.*

Jonathan wanda ke magana a taron kaddamar da littafin tuna lokacin da ya mika ragamar mulki ga shugaba Buhari, ya ce APC ta yi amfani da batun Boko Haram, sace matan Chibok da rage tallafin man fetur a matsayin dalilan da su ka sa a ka juyawa gwamnatin sa baya.*

Kazalika ya ce tambayoyi da a ke ta yi ma sa na dalilan da su ka saka ya bugawa shugaba Buhari waya ya amince da shan kaye da rashin zuwan sa kotu, sun sanya ya ga dacewar rubuta littafin.*

Ya ce bai ga laifin APC da ta yi amfani da dalilan ba wajen bata gwamnatin sa don ko shi kan sa da zai yi amfani da irin wadannan dalilan a siyasa.*

Shugaba Buhari wanda sakataren gwamnatin sa Boss Mustapha ya wakilta da sauran manyan baki da su ka halarci kaddamar da littafin a dakin taro na Hotel din Hilton a Abuja, sun yabawa Jonathan saboda amincewa da shan kaye.

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *