Saudiyya na azabtar da mata masu fafutuka – Amnesty

News

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yi zargin cewa Saudiyya tana azabtar da masu fafutuka da suka hada da mata da dama.

Fursunoni a Gidan Yarin Dhahban sun yi zargin cewa ana azabtar da su da lantarki da kuma zane su da bulala.

Saudiyya ta kama mata da dama masu fafutuka a farkon wannan shekarar da kuma fitattun malamai.

BBC ta tuntubi hukumomin Saudiyya don jin ta bakinta.

Sai dai wani jami’in Saudiyya ya shaida wa Mujallar Wall Street Journal cewa “masarautar ba ta goyon bayan azabtar wa kwata-kwata.”

Kungiyar Amnesty International da Human Rights Watch sun fitar da sanarwa a ranar Talata inda suka yi bayanin yadda ake azabtar da fursunonin.

Sanarwar Amnesty ta ce wasu masu fafutukar ba sa iya tsayawa da kafafunsu wasu kuma ba sa iya tafiya bayan da aka azabtar da su da lantarki da kuma yi musu bulala.

Ta kuma ce wata mata ta bayar da rahoton yadda wasu masu kula da wajen da ke rufe fuskokinsu suka dinga cin zarafinta da neman yin lalata da ita.

Ita ma sanarwar Human Rights Watch ta fitar da sanarwar yadda ake azabtar da mutane da lantarki da zane su da kuma tilasta musu wajen runguma da sumbatarsu, kamar yadda aka yi wa a kalla wasu mata uku da ake tsare da su.

File photo showing Saudi women's rights activist Aziza al-Yousef (27 September 2016)Hakkin mallakar hotoAFP
Image captionAziza al-Yousef is reportedly one of the women’s rights activists being held

An yi ta yabon Sarki Salman bn Abdulaziz Al Saud da dansa Yarima Mai jiran gado Muhammad bn Salman a bara sakamakon kawo sauye-sauyen ci gaban zamani da suka hada da dage dokar haramtawa mata tukin mota.

Amma masu suka suka ce a bangare guda kuma ana murkushe masu sukar masarautar, kuma kasar na fuskantar matsi daga kasashen duniya kan kisan Jamal Khashoggi a Santambul.

Saudiyya ta zargi wasu jami’ai da kisan amma ta yi watsi da zargin cewa yarima mai jiran gado ya san da shirin kisan dan jaridar.

Sai dai kuma hukumar CIA ta yi amanna Yarima Mohammed bin Salman ne ya bayar da umarnin kisan.

A ranar Talata Shugaba Donald Trump na Amurka a wata sanarwa da ya fitar ya kare dangantakar kasarsa da Saudiyya, duk da cewa ya ambaci cewa “ta iya yiwuwa” Yarima Muhammad ya san da kitsa kisan.

@www.bbc.com/hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *