An kashe fiye da Musulmi 50 a taron Maulidi

An injured person is taken to hospital in KabulHakkin mallakar hotoEPA
Image captionHarin shi ne mafi muni da aka kai birnin Kabul a watannin baya bayan nan

An kashe mutum fiye da 50 a wani harin kunar bakin wake da aka kai a dakin taron da ake gudanar da taron Maulidi a Kabul, babban birnin Afghanistan.

Jami’ai sun ce akalla mutum 83 ne suka jikkata lokacin da malaman addinin Musulunci suke taro a babban dakin da ke lardin PD15 domin tunawa da zagayowar ranar haihuwar annabi Muhammad (SAW).

Harin shi ne mafi muni da aka kai Kabul a watannin baya bayan nan.

Babu wanda ya dauki nauyin kai harin, sai dai kungiyar IS ta sha daukar alhakin hare-haren da aka kai a birnin a baya bayan nan.

Hare-haren da kungiyar Taliban ke yawan kai wa sun sa an kara tsaurara matakan tsaro, sai dai a wannan lokaci ta nesanta kanta da harin.

  • Da gaske ne Shehu Ibrahim Nyass ya bayyana a Maulidin Abuja?
  • Hotunan bikin Maulidin Shiekh Ibrahim Nyass a Abuja

Akalla mutum 1,000 ne a dakin taron lokacin da aka kai harin, in ji jaridar Tolo.

1TV News ta ambato jami’an kula da lafiya na cewa mutum 24 sun ji mummunan rauni.

Wani manajan da ke kula da dakin taron ya ce dan kunar bakin aken ya tashi bam din da ke jikinsa a tsakiyar masu bikin Maulidin.

Shugaban kasar Afghanistan, Ashraf Ghani, ya yi alla-wadai da hari da ya bayyana da laifin da ba za a taba yafe wa ba, ya kuma ayyana zaman makoki a fadin kasar.

Afghan soldier at Kabul hospitalHakkin mallakar hotoEPA
Image captionYawaitar hare-haren ya sa an tsaurara tsaro

Kungiyar IS ta ce ita ce ta kai hari biyu a Kabul a watan Agusta wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Kazalika ita ta kai harin da ya halaka mutane da dama da ke kada kuri’a lokacin zaben majalisar dokokin kasar a watan Oktoba.

Sai dai a kwanakin baya bayan nan an rika yunkurin sulhu domin kawo karshen irin wadannan hare-hare da aka kwashe shekara da shekaru ana kai wa kasar.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *