Kotu ta dakatar da majalisa daga binciken Ganduje

News

Wata babbar kotun jihar Kano da ke Najeriya ta dakatar da majalisar dokokin jihar daga binciken da take yi a kan zargin da ake yi wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje na karbar hanci.

A watan jiya ne majalisar dokokin ta kaddamar da kwamitin domin bincike kan bidiyon da ya nuna Gwamna Ganduje yana karbar miliyoyin dala daga wurin wasu ‘yan kwangila.

Sai dai ranar Litinin, kotun ta bukaci kwamitin ya dakatar da binciken zuwa wani lokaci da za ta saurari karar da wata kungiyar lauyoyi ta gabatar mata.

Shugaban kungiyar Barrister Zubairu Muhammad ya yi zargin cewa majalisar dokokin jihar Kano ba ta da hurumin gudanar da bincike a kan Gwamna Ganduje kasancewar yana da rigar-kariya.

A cewar kungiyar, binciken da kwamitin ke yi tamkar cin zarafin kundin tsarin mulkin Najeriya ne.

Da ma dai ranar Talata kwamitin majalisar dokokin ya tsara zai kebe da lauyoyin dan jaridar da ya fitar da hotunan bidiyon da kuma lauyoyin gwamna Ganduje don nazarin hotunan tare da kwararru da nufin tantance sahihancinsu.

Sai dai shugaban kwamitin Alhaji Bappa Babba Dan Agundi ya shaida wa BBC cewa ba a gabatar musu da hukuncin kotun ba, yana mai cewa “a matsayina na tsohon ma’aikacin kotu za mu dauki mataki da zarar an gabatar mana da hukuncin.”

Kotun dai ta tsayar da ranar 12 ga watan Nuwamba don sauraron karar.

@www.bbc.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *