‘Yan fashi sun ‘kashe mutum 10’ a Birnin Gwari

Birnin Gwari
Image captionYankin Birnin Gwari

Kungiyar wanzar da tsaro da kyakkyawan shugabanci ta Birnin Gwari ta ce ‘yan fashi sun afkawa wasu kauyukka hudu a yankin, inda suka kashe akalla mutum 10 a ranar Talata.

Kauyukan sun hada da Mashigi da Dakwaro a gundumar Kakangi a yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta ce an kai harin ne a mazabar wani dan majalisar tarayya Hon. Hassan Adamu Shekarau wanda ya gabatar da wani kuduri mai sosa rai gaban majalisar wakillan kasar kan rashin tsaro a yankin nasa ‘yan sa’o’i bayan da ya gabatar da kudurin.

Rahotanni sun ce da misalin karfe biyar na ranar Talata ne maharan suka afkawa garin kuma sun shafe sa’o’i fiye da uku a cikin kauyukan.

Wani dan banga mai suna Malam Umar ya shaida wa kamfanin yada labarai na PR cewa an gano gawawwakin “mutum 10 a yanzu.”

Dan majalisar Hon. Hassan ya tabbatarwa da BBC faruwar al’amarin.

Sai dai ya ce akalla mutum takwas ne suka rasa rayukansu sanadiyyar harin.

Rahotanni sun kuma ce ‘yan fashi sun kona gidaje da dama da kuma kayan abinci.

An tura da jami’an tsaro da kuma ‘yan banga zuwa wuraren da lamarin ya faru domin tabbatar da adadin wadanda aka kashe.

Lamarin na zuwa ne bayan harin da ‘yan fashi suka kai kauyen Gwaska, inda suka hallaka mutum fiye da 40.

Haka kuma a baya-baya nan ne ‘yan bindiga suka sace mutum fiye da 80 a kan wata babbar hanya da ta hada arewaci da kudancin kasar a yankin Birnin Gwari.

A farkon watan da muke ciki ne Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarnin kafa sansanin soji na dindin a yankin.

Sai dai har yanzu ‘yan bindigar na ci gaba da kai wa mazauna yankin hari.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *