GUZURIN RAMADAAN: Falalar Dake Cikin Azumi

 

Daga Mahmud Isa Yola

Fitowa na 01

Bismillahirrahmanirrahim,

Ina yi mana maraba da zuwan wata mai alfarma wato watan Ramadaan. Muna Godiya ga Allah SWT da ya tsawaita rayuwar mu zuwa wannan lokaci, Allah Ya karbi Ibadunmu. Bayan haka, Azumi daya ne daga cikin manyan ibadu a wurin Allah SWT kaman yadda ya zo a Qur’ani da Hadisan Manzon Allah SAW. Ga wasu daga ciki:

* Idan watan Ramadaan ya fara, ana rufe kofofin wuta kuma ana bude kofofin Aljanna, kuma ana daure Shedanu. [ Bukhari Fat’h 3277]

* Azumtan watan Ramadaan daya yake da azumtan watanni goma. [Musnad Imam Ahmad, 5/280]

* Duk wanda ya azumci watan ramadaan da imani tare da yakinin samun yardar Allah, za a gafarta masa dukkan zunuban sa da suka gabata. [Bukhari, GUZURIN7]

* Azumi bai da ibadan da ya yi gogayya da shi a lada, kuma ba a dawo da addu’an mai azumi. [Al-Bukhari, fat’h 1904]

* Mai azumi yana da lokuta guda biyu na jin dadi; daya lokacin da yayi buda baki, na biyu kuma lokacin da ya gamu da Ubangijin sa yana murna akan azumin da ya yi. [Silsilatul Saheha 1797]

* Azumi zai yi ceto a ranar hisabi inda zai ce: “Ya Ubangiji, na hana shi abincin sa, da abubuwan da yake bukata bayyanannu a lokacin yini, a bar ni in cece shi” [Sahehul Targib, 1/407]

* Warin bakin mai azumi ya fi kamshi a wurin Allah SWT akan turaren miski [Sahihu Muslim, 2/807]

* Azumi kariya ne da yake nesantar da mutum daga azabar wutar jahannama. [Saheehul Jaami 3880]

* Duk wanda ya yi azumi na kwana daya saboda Allah, Allah SWT zai nesantar da fuskar sa tazarar shekaru 70 daga wuta. [Sahihu Muslim 2/808]

* Duk wanda ya yi azumi na kwana daya don neman falalar Ubangiji, kafin ya buda baki ya koma zuwa ga Allah, to zai shiga Aljanna [Saheehul Targib 1/412]

* A cikin Aljanna akwai wata kofa mai suna Al’Rayyan, babu wadanda za su shige ta sai masu azumi. [Sahihul Bukhari 1797]

* A cikin watan Ramadan ne Allah SWT ya saukar da AlQur’ani, kuma a cikin ta ne daren Lailatul’Qadr yake, wanda Allah SWT ya ce daren ya fi watanni dubu.

* Duk lokacin shan ruwa bayan azumi, Allah yana zaban bayin sa wadanda zai ‘yanta daga wuta. [Saheehul Targhib 1/419].

WANNAN RUBUTU NA GUZURIN WATAN RAMADAN ZAI CIGABA DA ZUWA MUKU A SHAFIN RARIYA, TARE DA MAHMUD ISA YOLA.

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *