Duk Musulmin Da Allah Ya Tsawaita Rayuwarsa Zuwa Ramadan, Hakika Ya Dace Da Babban Rabo, Inji Ustas Nuruddeen Khamees

 

An bayyana Watan Ramadan a matsayin wata babbar baiwa da Allah SWT ya yi wa al’ummar Musulmi da ita, kuma dukkanin wani Musulmi da Allah ya tsawaita rayuwar shi zuwa Watan Ramadan to shakka babu Allah yayi mishi wata gagarumar baiwa wacce wasu jama’a da dama basu samu irin ta ba.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin wani Malamin Addinin Musulunci mazaunin garin Kaduna, mai suna Ustas Muhammad Nuruddeen Khamees lokacin da yake tsokaci akan falalar Watan Ramadan, a yayin wata tattaunawa da manema labarai da yayi a gidan shi dake garin Kaduna.

Ustas Nuruddeen Khamees ya cigaba da cewar, hakika Allah ya zabi Watan Ramadan akan sauran Watannin Musulunci 11, domin a cikin watan ne aka saukar da Al Kur’ani mai girma, sannan dukkanin wani aikin Alkhairi da Mutum yayi a cikin Watan Ramadan Allah yana ribanya shi ninkin ba ninkin, sannan a cikin wannan wata ne Allah ya samar da wani Dare mai suna Daren Lailatul Kadari, wanda wannan dare daya yana matsayin Watanni dubu ne, wato idan aka dauki lissafi Daren Lailatul Kadari na matsayin shekaru 84 ne, lallai wannan ba karamar baiwa ce.

Malamin ya cigaba da cewar, ya inganta a hadisi Manzon Allah SAW ya bayyana cewar Mala’ika Jibirilu yayi Addu’a sannan ya bukace shi da yace Amin, Addu’ar kuma ita ce Allah ya la’anci wanda duk ya riski Watan Ramadan sannan ya gagara yin aikin da Allah zai gafarta mishi a ciki, sannan Annabi yace amin, dalilin wannan la’anta kuwa shine irin garabasa da ke cikin Watan Ramadan amma ace Mutum ya kasa aiwatar da aikin da zai samu gafara a ciki, babu shakka wannan Mutumin ya tabe.
Saboda haka ya bukaci Jama’ar Musulmi da kada su yi sake da wannan dama da Allah ya basu, su dage wajen yawaita Istigifari da karatun Al Kur’ani da yawaita Sadaka da Nafiloli domin dacewa da samun garabasa da ke cikin wannan wata.

Ustas Muhammad Nuruddeen Khamees ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa Musulmi da cewar, su ji tsoron Allah Ubangijin su kada su kara tsawwala farashin kayayyakin su da nufin cin kazamar riba a cikin Watan Ramadan, ya kamata ‘yan kasuwar mu su gane Watan Ramadan wata ne na neman Lada da dacewa a Lahira, ba wata ba ne na tara abin duniya, kamata yayi a ce cikin Watan Ramadan Jama’ar Musulmi harma da wadanda ba Musulmi sun samu sauki ta fuskar kayayyakin masarufi, domin a wasu kasashe da suka cigaba na Musulmi ana zabtare farashin kayayyakin masarufi domin su samu sauki a cikin watan, sannan su kansu ‘yan kasuwan su dace da samun gagarumar lada a wajen Ubangijin su.

Dangane da batun Malamai masu gabatar da Tafsiri a lokacin Watan Ramadan kuwa, Malamin ya ja hankalin su tare da kira a garesu da yin koyi da tsarin gudanar da tafsiri irin yadda sanannen Malamin Addinin Musulunci nan Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya gudanar, wato gabatar da Tafsiri cikin tsentseni da Ikhlasi, ba tare da kaucewa ainihin tsarin tafsirin ba, wanda wannan shine dalilin da yasa Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya jima da rasuwa amma har yanzu karatun shi ke da tasiri matuka, saboda ina kira ga Malamai masu gabatar da tafsiri a wannan wata na Ramadan, su tsaya akan karantawa bisa ga tsari na Kitabu Was Sunnah, domin neman yarda a wajen Allah SWT da kuma dacewa da samun rahama a ranar Kiyama.

@Rariya

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *