Russia 2018: Super Eagles ta fitar da sunayen ‘yan wasa 30

Nigera Super Eagles 30-man listHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionA ranar 4 ga watan Yuni ne Najeriya za ta aiikewa hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) sunaye ‘yan wasa 23

Kocin tawagar kwallon kafar Najeriya Gernot Rohr ya fitar da kwarya-kwaryar sunayen ‘yan wasa 30 wadanda daga cikinsu ake saran za su wakilci kasar a Gasar Cin Kofin Duniya wanda za a fara a watan Yuni a kasar Rasha.

Cikin ‘yan wasan akwai tsohon dan wasan Chelsea Mikel Obi da Ahmed Musa da Odion Ighalo da Victor Moses da dai sauransu.

A cikin wadannan ‘yan wasan ne kocin Super Eagles din zai zabi ‘yan wasa 23 wadanda za a tafi kasar Rasha da su don fafatawa a gasar wadda za a fara ranar 14 ga watan Yunin bana.

A ranar 4 ga watan Yuni ne kocin zai aikewa hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) sunaye ‘yan wasa 23.

Najeriya tana rukunin D ne wanda ya kunshi kasashen Croatia da Iceland da kuma Argentina.

A shirye-shiryen tunkarar gasar, tawagar kasar za ta yi wasannin sada zumunci da DR Congo a ranar 25 ga watan Mayu, sai karawa da Ingila a ranar 2 ga watan Yuni.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *