APC ‘ta rabu biyu’ a wasu jihohi

Gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari da tsohon Gwamnan Sokoto Malam Yahaya Abdulkarim suna kada kuri'aHakkin mallakar hotoA B KAURA
Image captionGwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari Abubakar yana kada kuri’ar zaben shugabannin APC

Rikicin cikin gida a wasu jihohi da dama na APC ya yi tasiri a zaben shugabannin jam’iyar a mataki na kananan hukumomi.

Wasu bangarori na APC a jihohin Kano da Zamfara da Adamawa sun gudanar da nasu zaben na daban na shugabanin jam’iyyar a kananan hukumomi.

A ranar Lahadi ne bangaren Kwankwasiyya suka gudanar da nasu zaben a Kano bayan daya bangaren da ke mulki a jihar ya gudanar da zaben a ranar Asabar.

Bangaren Sanata Marafa da ke wakiltar Zamfara ta tsakiya sun yi ikirarin gudanar da nasu zaben a ranar Asabar, daidai lokacin da bangaren APC da ke mulki a jihar ya gudanar da nasa zaben.

Uwar Jam’iyyar dai ta sha nanata cewa kan ‘yayanta a hade yake, amma har yanzu babu sanarwa da ta fitar game da rabuwar kan da aka samu a zaben shugabannin jam’iyyar.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin shugabannin uwar Jam’iyyar amma ba su amsa sakwannin da aka tura ma su ba.

  • Zaben shugabannin APC ‘ya bar baya da kura’
  • Wasu jiga-jigan APC sun gargadi Buhari da kuma jam’iyyar

Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo daya daga cikin shugabannin tafiyar Kwankwasiyya ya shaida wa BBC cewa jinkirin da suka samu wajen samun fom ne ya sa suka dage gudanar da zabensu zuwa ranar Lahadi maimakon Asabar.

A zaben shugabannin APC a matakin mazabu ma da aka gudanar a makon da ya gabata, bangaren Kwankwasiyya sun gudanar da nasu zaben ne na daban.

Bangaren Sanata Marafa, da ke hamayya da bangaren gwamnati da ke mulkin jihar Zamfara sun yi zargin cewa an shirya gudanar da zaben shugabannin APC ba tare da tuntubarsu ba, dalilin da ya sa suka shirya nasu zaben na daban.

“Mutanenmu sun fito suna sha’awar takara amma gwamnati ta zo tana dauki-dora” kamar yadda kakakin bangaren Sanata Marafa, Muhammad Bello Soja Bakyasuwa Maradun ya shaida wa BBC.

Yadda aka yi zaben shugabannin APC a ZamfaraHakkin mallakar hotoA B KAURA
Image captionYadda aka yi zaben shugabannin APC a Zamfara

Sai dai kuma shugaban kwamitin gudanar da zaben da gwamnati ta nada Hon. Sanusi Garba Rikici ya ce ba ya da wata masaniya da wani zabe na daban a jihar, illa wanda ya jagoranta.

Ya ce sun gudanar da zaben a kananan hukumomi 14 na Zamfara ba tare da wata matsala ba tare da musanta ikirarin da bangaren Sanata Marafa suka yi game da hana ma su sayen fom.

Rahotanni sun ce wani bangare na APC a jihar Adamawa ya gudanar da zaben shugabanninsa na daban a jihar, kuma dukkanin bangarorin na ikirarin sahihancin shugabanninsu da suka zaba.

APC dai ta rabu biyu a Adawama tsakanin bangaren Sakataren gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da kuma bangaren tsohon Sakataren gwamnati Babachir David Lawal.

Rahotanni a jihar Filato ma sun ce an dage zaben shugabannin jam’iyyar a karamar hukumar Langtang ta kudu sakamakon rikici tsakanin magoya bayan Ministan wasanni da ci gaban matasa Barista Solomon Dalung da kuma bangaren gwamnan jihar Simon Lalong.

Rikicin bangarori a jihohin APC da ke mulki a Najeriya ya kara fito da girman kalubalen da ke gabanta a zaben 2019.

Kuma masharhanta siyasa na ganin rigingimun jam’iyyar da ta ke fama da su a jihohi na iya yi wa jam’iyyar illa sosai a zaben 2019.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *