Abubuwa biyar da za su iya hana PDP tsayar da Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jigawa Sule LamidoHakkin mallakar hotoAFP
Image captionSule Lamido zai yi takara a PDP da wasu manyan ‘yan siyasa na jam’iyyar

Tsohon Gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido na cikin manyan ‘yan siyasar Najeriya da suka bayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta PDP a zaben 2019.

Sai dai kuma ana ganin jam’iyyar PDP da tsohon gwamnan zai nemi ta tsayar da shi, ba za ta yi sakaci ba wajen zaben tumun-dare a matsayin dan takararta, a yunkurin da take na kwace mulki daga hannun APC.

A shekarar 2015 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kayar da Goodluck Jonathan na PDP, kuma tun daga lokacin ne jam’iyyar ke ta fadi-tashin ganin ta farfado. A don haka babban kalubalen da ke gaban PDP shi ne tsayar da dan takarar da zai kawar da gwamnatin APC ta shugaba Buhari a zaben 2019.

Za mu rinka yin nazari kan kalubalen da masu neman takarar shugabancin kasar za su iya fuskanta, inda a wannan karon muka duba muhimman abubuwa biyar da za su iya zama barazana ga takarar Sule Lamido a jam’iyyar ta PDP:

1. Yana fuskantar shari’a

Alhaji Sule Lamido na fuskantar shari’a kan zargin almundahana da kudaden al’umma a lokacin da yana gwamnan Jigawa.

A 2015 ne Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta gurfanar da shi a kotu da wasu ‘ya’yansa biyu kan laifuka 27 da suka kunshi sama da fadi da kudaden jama’a.

Ko da yake tsohon gwamnan ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake ma sa, kuma har yanzu kotu ba ta kai ga yanke hukunci kan shari’ar ba.

Amma wasu masu sharhi na ganin wannan zai iya zama matsala ga aniyar Sule Lamido ta samun tikitin jam’iyyar PDP.

Suna ganin PDP ba za ta yarda ta tsayar da dan takarar da za ta zo tana kokarijn kare wa ba, musamman ganin cewa ba a san yadda shari’ar za ta kaya ba.

Jam’iyyar za ta nemi ta tsayar da dan takarar da ba ya da wani kalubale a kotu, domin kada ‘yan adawa su yi amfani da wannan damar su bata tafiyar jam’iyyar, musamman ganin yadda batun cin hanci da rashawa ya taka rawa a zaben 2015 wanda jam’iyyar ta sha kaye.

Sule LamidoHakkin mallakar hotoPIUS UTOMI EKPEI
Image captionSule Lamido ya rike mukaman siyasa da yawa a Najeriya

2. Ra’ayin kansa

Masharhanta siyasar Najeriya na kallon Sule Lamido a matsayin mutum da ke da ra’ayin kansa. Kuma ba kasafai ake iya tursasa shi ba.

Suna ganinsa a matsayin mutum da yake nuna isa, musamman yadda yake nuna ba ya da wani uban gida da zai iya yi masa hanzari.

Wasu kan yi amfani da yadda rayuwa ta kasance tsakaninsa da tsohon mai gidansa marigayi Abubakar Rimi, wurin nuna cewa yana da nuna isa.

Amma daga bisani tsohon gwamnan ya sasanta da mai gidan nasa, kuma ya bayyana Rimi a matsayin wani jigo na siyasa a Najeriya.

Sai dai wasu na ganin za a iya cewa Olesegun Obasanjo unban-gidansa ne kuma yana fada masa ya ji.

Ita dai jam’iyyar PDP za ta so ta tsayar da dan takarar da za ta iya tankwasawa, tare da mutunta bukatunta, musamman ganin halin da ta smau kanta a ciki.


Masu neman takara a PDP

 • Alhaji Atiku Abubakar
 • Ayo Fayose
 • Malam Ibrahim Shekarau
 • Sule Lamido

Ahmed Makarfi (bai bayyana ba kawo yanzu)


3. Karbuwa a Arewa

Ganin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ke da magoya baya a arewacin Najeriya, PDP za ta so ta tsayar da dan takarar da zai iya ja da shugaban.

Sule Lamido, yana cikin manyan ‘yan adawa da ke sukar gwamnatin Shugaba Buhari da jam’iyyar APC.

Amma wasu na ganin a matsayinsa na gogaggen dan siyasa a Najeriya, yana iya adawa da Buhari amma ta hanyar da tsohon gwamnan zai samu farin jinin jama’a.

Kamar yadda wasu suka bada misali da irin mamayar da Donald Trump ya yi a Amurka wajen sukar gwamnati ta hanyar da mutane suke so.

Yadda tsohon gwamnan yake adawa da Buhari, wasu na ganin ya kara jawo masa bakin jini a tsakanin wasu ‘yan arewar.

Duk da ana ganin farin jinin Shugaba Buhari ya ragu a arewa amma wasu na ganin Sule Lamido ba ya da karbuwar da har zai iya ja da shi.

PDP za ta yi kokarin tsayar da dan takarar da zai yi gogayya da Buhari wanda zai wawuri wasu daga cikin kuri’un da shugaban ya samu a 2015.

Masu sharhi na ganin duk dan takarar da zai ka da Buhari, to wajibi ne ya samu kuri’u masu gwabi a arewa.


Wane ne Sule Lamido

Sule Lamido tsohon gwamnan JigawaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionSule Lamido na sahun gaba wurin adawa da Buhari da APC a arewacin Najeriya
 • An haife shi a shekarar 1948 a garin Bamaina, Karamar Hukumar Birnin Kudu a Jigawa
 • Shekararsa 69
 • Tsohon dalibin Barewa College ne
 • Tun yana matashi ya ke siyasa
 • An zabe shi dan majalisa a jamhuriya ta biyu a karkashin jam’iyyar PRP
 • Yana cikin mutanen farko da suka kafa jam’iyyar PDP
 • Ya kasance Ministan harkokin wajen Najeriya daga 1999-2003
 • Ya kasance Gwamnan Jigawa daga 2007 zuwa 2015
 • An taba daure shi a zamanin mulkin Janar Sani Abacha
 • EFCC ta gurfanar da shi Kotu kan zargin halatta kudaden haram, zargin da ya musanta

4. Alakarsa da gwamnoni

Jam’iyyar PDP na kokarin farfado da martabarta ga ‘yan Najeriya ne a yanzu bayan ta sha kaye a zaben 2015 bayan shafe shekara 16 tana mulki, lamarin da ya so ruguza jam’iyyar.

Wasu na ganin gwamnonin PDP ne za su kasance alkiblar jam’iyyar, musamman wajen zaben dan takarar shugaban kasa a babban taronta na kasa.

Kuma duk wanda jam’iyyar za ta tsayar dole sai ya samu karbuwa da goyon bayan gwamnonin jam’iyyar.

Amma masharhanta na ganin alakar tsohon gwamnan na Jigawa da gwamnonin PDP tana da rauni, saboda ba ya kan mulki yanzu, kuma yawancin gwamnonin ba ‘yan arewa ba ne.

Haka ma alakarsa da Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ba tada kyau sosai. Kuma ana ganin har yanzu Mr Jonathan na da karfi a jam’iyyar.

Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo duk da bai fito ya bayyana aniyarsa ba ta tsayawa takarar shugaban kasa, amma ana ganin idan har ya fito ya nuna yana so, to gwamnonin PDP na iya mara ma shi baya.

Tarihin Sule Lamido

Gagarumin dan siyasa

1948

Aka haife shi a garin Bamaina a jihar Jigawa

 • 1979 Ya zama dan majalisar tarayya a Legas a karkashin PRP
 • 1999 – 2003 Ya zama ministan harkokin wajen Najeriya a karkashin jam’iyyar PDP
 • 2007 – 2015 Ya mulki jihar Jigawa a matsayin gwamna a PDP
 • 2018 Ya fito takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP
Getty

5. Karfin Iko

Kwace mulki daga jam’iyyar APC mai mulki shi ne babban kalubalen jam’iyyar PDP.

Jam’iyyar adawar ta Najeriya za ta so ta tsayar da dan takara mai kudi da karfin fada aji, wato dan takarar da ke rike da wani madafin iko.

Za ta so ta tsayar da dan takarar da zai iya tallafawa sauran ‘yan takararta da kuma jam’iyyar domin yakar APC a zaben gwamnoni, ‘yan majalisa da na shugaban kasa.

Hidimar daukar nauyin wakilan jam’iyya a babban taron fitar da dan takara, harka ce da ke bukatar kudi, kuma hakan zai yi tasiri ga zaben dan takarar jam’iyyar.

Masana siyasa na ganin PDP ba za ta so ta tsayar da wanda za ta sha wahala da shi ba musamman wajen yakin neman zabe da hidimar magoya baya.

Ana ganin Sule Lamido ba shi da karfin yin hakan, musamman ganin ba ya rike da wani mukami yanzu. Kuma za a cewa zai fuskanci kalubale wurin nemo gudummawa da jan hankalin masu hannu da shuni.

 • Abubuwa uku da suka sa Buhari neman wa’adi na biyu
 • Su waye za su ja da Buhari a zaben 2019?. BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *