Ma’adanai na hada kan Fulani makiyaya da manoma a jihar Filato

Masu hakar ma'adinin kuza Barikin Ladi
Image captionManoma da Fulani makiyaya na aiki tare a wata sabuwar mahakar ma’adanai

Sauyin yanayi ya sa zaman doya da manja da ake yi tsakanin manoma da kuma makiyaya masu kiwo ya rikide zuwa rikici tsakanin kabilu.

Sai dai ko aiki tare zai shawo kan yawan bukatun mutanen wannan zamani da kuma magance rikice-rikice masu nasaba da kabilanci, wakiliyar BBC Stephanie Hegarty ta yi nazari a kan batun.

Yayin da rana ta fara faduwa a tsaunukan Jos, shanu na sauka daga saman wurin zuwa kasa inda akwai duwatsu suna bin wata hanya da suka saba bi a cikin shekaru aru-aru domin neman abinci.

A cikin wannan yanayi na zaman lumana, babu wani da zai yi tunanin cewa al’ummomin wannan yankin da ke tsakiyar Najeriya na fada da juna idan ban da a baya-baya nan.

Sai dai rikicin na cikin manyan tashe-tashen hankulan da duniya take fama da su a wannan lokaci.

Wannan layi ne

Ana ci gaba da samun kwararowar hamada a arewacin Afirka, abin da kuma ke shafar filaye masu ciyayi, lamarin da ke hadassa rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma.

“Al’ummata za ta kashe su,” a cewar Henry Botson, mai shekara 30 wanda dan kabilar Berom.

Yana zaune ne a Barikin Ladi, da ke jihar Filato, inda aka samu barkewar tashin hankali tsakanin al’ummarsa da makwabtansu a shekarar 2011.

“Kuma idan muka shiga yankinsu, za su kashe mana mutanenmu.”

Mista Botson gajere mutum ne mai kiba, amma ba sosai ba, kuma yana sanye da hula koriya kuma ya rataya bindiga kirar AK-47 a wuyansa.

Sai dai wannan yana cikin matsalolin da ake fuskanta.

Tun bayan da aka kifar da gwamnatin Libya, aka samu matsalar kwararar bindigogi a yankin yammacin Afirka, kuma ana shigo da yawancinsun Najeriya.

Wasu mutane a Dogo Nahaw, wani kauye a kudancin Jos, sun taru domin binne gawawwakin 'yan garinsu da aka kashe a lokcin rikicin adini a watan Maris a shekarar 2010Hakkin mallakar hotoSTR/AFP/GETTY IMAGES
Image captionAn binne gawawwakin mutane da dama a cikin babban rami irin wannan a lokacin tashin hankali kauyen Dogo Nahawa

A cikin shekaru biyar da suka gabata dubban mutane ne suke hallaka a tashin hankali mai nasaba da kabilanci da aka yi a Barikin Ladi, mai nisan Kilomita 268 da birnin Abuja.

Adadin rayukan da ka rasa a tsakiya da kudancin Najeriya ya fi dubu 2,000 a tsakanin shekarar 2011 da 2016, a cewar kungiyar agaji ta Crisis International.

  • Ganduje ya gayyaci makiyaya su koma jihar Kano
  • Ba za mu bai wa Fulani wurin kiwo ba — Gwamnan Benue

“Wani Bafulatani ne ya lalata gonar wani dan kabilar Berom, shi kuma mutumin sai ya kashe shanun Bafulatanin da kuma yaransa da ke kula da shanun ,” a cewar Farouk Abubaker, wanda shi ma Bafulatani ne.

“Muna kallonsu a matsayin mutane masu mugunta. Muna kallonsu a matsayin mutane da ba su da imani saboda sun kashe mana yara kanana da mata, ciki har da mata masu juna biyu.”

“Akwai abubuwa da dama marasa kyau da suka faru – amma duk wannan ya koma tarihi yanzu .”

Wannan dai ya biyon bayan cewa komai ya lafa a cikin shekaru biyu da suka gabata.

An dai gano ma’adanin kuza (Tin), a lokacin da farashinsa a kasuwanin duniya ya tashi sakamakon bukatar da masana’antu masu kera kayan latoroni suke yi masa.

A yanzu Abubakar da Mr Botson suna cikin aiki tare ne a mahaka daya, inda suke tono kasa domin neman ma’adanin kuza a wurin da Fulani makiyaya da shanunsu suke bi a kowace rana.

Wani mai hakar ma'dinai zai shiga cikin wata mahaka a Barikin Ladi
Image captionAiki ne mai hadari: Mutane da dama sun mutu bayan da ramin da suke ciki ya rufta

Aiki ne mai hadari sosai, mutane da dama sun rasa rayukansu a duk lokcin da mahakar ta ruguje a kan haka ba su da wani zabi illa su yadda da junansu.

“Abin ya ba ni mamaki ,” a cewar Mr Botson. “Ban taba tunanin cewa za mu iya aiki tare ba, mu zauna mu yi magana da juna kuma mu yi wani abu kamar wannan.”

Ma'aikata na neman ma'adinin ta hanyar wanke kasa
Image captionMa’aikata na neman ma’adanin ta hanyar wanke kasa

Tun da asuba daruruwan maza da mata da kuma yara suke tururuwa zuwa wurin hakar ma’adanin kuza.

A ko ina a mahakar, Fulani na aiki tare da Berom, sai dai ko ya hakan ya faru?

A lokacin da aka zabi sabon gwamnan jihar Filato a shekarar 2015, ya yi alkawarin kawo karshen rikice-rikicen da ake fuskanta tsakanin Fulani makiyaya da ‘yan kabilar Berom.

Sai dai a lokacin da ya dauki Joseph Lengmang, mai shekara 42, a matsayin shugaban hukumar tabbatar da zaman lafiya ta jihar, mutane da dama sun nuna shaku a kan ko matashin zai samu kwarin gwiwar kiran shugabannin yankin su zauna da juna a kan teburin shawara.

“Gwamnati nan ta gaji wani yanayi na tashin hankali ,” in ji Mr Lengmang .

“Abu ne da ya dauki tsawon lokaci. Akwai lokacin da muka fara tada jijiyoyin wuya kamar za a samu barkewar tashin hankali.”

“Sai dai mun samu kwararru masu shiga tsakani…kuma a karshe mun cimma sulhu”.

Wani taro na hukumar tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a jihar Flato a watan disembaHakkin mallakar hotoPPBA/FACEBOOK
Image captionTaron hukumar tabbatar da zaman lafiya mai dorewa ta jihar Filato

Sai dai ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula tsakanin Fulani makiyaya da manoma a tsakiyar Najeriya. Kuma an kashe mutum shida a Barikin Ladi a baya-bayan nan.

Akwai mutane da dama da suka dora alhaki a kan ‘yan siyasa domin neman goyon bayan mutane yayin da babban zaben Najeriya ke kara kawo jiki.

Sai dai Mr Lengmang ya yi amannar cewa ayyuka irin wannan da ake yi a Barikin Ladi za su taka rawa sosai wajen tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

“Sun ko yi darasi daga abubuwan da suka faru baya… Idan aka samu barkewar tashin hankali kowa ne yake asara”.

Thomas Johji na cikin mutanen da suka gano wurin da ma’adanin kuza yake a watanin da suka gabata.

Wuri ne da ke tsakiyar inda Fulani makiyaya suke kiwo da dabbobinsu, a kan haka abu ne mai muhimmanci a samu hadin kan makwabtansu Berom.

Shi ya sa suka gayyace su a kan su zo su yi aiki tare.

Shekarun Mr Johji ba su kai 30 ba, kuma ya kasa tuna yadda rikicin ya fara.

“Yanzu muna iya bacci a cikin daji tare da Fulani, mu tashi tare mu yi wasa tare,” in ji shi.

“Fulani sun manta da abin da ya faru kuma mu ma muna kokarin ganin cewa mun manta da abin da ya faru.”

Wani ma'aikaci na hutawa bayan ya yi aiki a mahakar Barikin Ladi mine
Image captionWani ma’aikaci na hutawa bayan ya yi aiki a mahakar Barikin Ladi Mine
Wata yarinya ta dauki kasa a ka a mahakar Barikin Ladi
Image captionWata yarinya ta dauki kasa a kai a mahakar Barikin Ladi Mine
Wata mata na dauke da kwano a mahakar Barkin Ladi
Image captionWata mata na dauke da kwano a mahakar ma’adanin Barkin Ladi

Sai dai akwai wadansu da za su dauki lokaci kafinsu manta da abin da ya faru, akwai rashin yarda tsakanin kabilun biyu.

Wata ‘yar kabilar Berom da ke aiki a wata mahakar kuza da ke kusa ta ce ba ta iya sakewa a cikin Fulani.

Ta ce ta kasa yarda da mutanen da ta ce sun kashe mata ‘yan uwa da abokai.

“Ko a yanzu muna cikin fargaba – amma komai yana hannun Ubangiji,” a cewarta.

Ta kara da cewa dole ne ya sa ta fito “Idan ka tsaya a gida, shin ta yaya za ka ci abinci?”

Mr Lengmang ya amince da cewa kawo a yanzu ba a samu zaman lafiya mai dorewa ba a jihar Filato.

“Akwai wadansu korafe-korafen da ba a dauki mataki akansu ba, a hukumance kuma akwai rashin yarda tsakanin kabilun,” in ji shi.

“Ya kamata a hada kowa da kowa a tsarin hakar ma’adanai.”

Idan ma’adanin kuza ya kare, watakila a sake fuskantar tashin hankali mai nasaba da albarkatun kasa.

Hukuma ta fara duba hanyoyin ba da horo a kan yadda za a shawon a kan ringingimu ko kuma yadda za a karfafa wa bangarori gwiwa a kan yadda za su sa hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya kafin su fara aiki a wurin da aka gano ma’adanin.

Sai dai Malam Abubakar ya yi amannar cewa bangaren ya fara yin wani abu domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

“Hakar ma’adanai na tabbatar da hadin kai da fahimta juna a tsakin kabilu, kamar yadda kwallon kafa take yi,” in ji shi.

“Ina farin ciki da haka kuma fata na shi ne za mu ci gaba da zama lafiya da juna.”

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *