‘Yan Afirka na yakar wariyar launin fata ta hanyar amfani da kwallon kafa

Yan wasan All black FC sun daga yatsa a hoton da suka daukaHakkin mallakar hotoALL BLACK FC
Image caption‘Yan wasan kwallon kafa na All Black FC wanda daga bisni Sinawa da Hong Kong da kuma sauran kabilu marasa rinjaye suka shiga ciki

Ba kasafai ‘yan yankin Hong Kong, suke buga wasan kwallon kafa da ‘yan cirani ba .

Duk da cewa wannan ba abin mamaki bane amma kashi 1 bisa uku na Sinawa dake Hong Kong basa son zama kusa da sauran kabilu a cikin motocin safa-safa ko yin makobtaka da su, haka kuma ba sa son yaransu suna zuwa makaranta tare da ‘ya’yan wasu kabilu ba, kamar yadda wani boncike da kungiyar Unison ta yi ya nuna.

Sai dai ko wasan kwallon kafa zai iya kawar da wannan matsala?

Tun a shekarar a 2016 ne wata tawagar kwallon kafa ta ‘yan ci rani da ake kira All Black FC ta soma yin wannan gwaji yayinda ‘yan wasan kungiyar suke kokarin sajewa da ‘yan yankin tare da kuma inganta kimar ‘yan Afrika a yankin.

Medard Privat Koya wanda tsohon dan wasan jamhuriyar tsakiyar Afrika ne shi ne wanda ya kafa kungiyar.

A lokacin akasarin ‘yan wasansa na farko masu neman mafaka ne daga Afrika, amma yanzu yawan ‘yan wasan ya karu bayan wasu ‘yan China da kabilu marasa rinjaye suka shiga cikin kungiyar .

“Wasan kwallon kafa zai iya hada kawunanmu,” in ji shi .

Haka kuma wasan na hana zaman kashe wando, saboda masu neman mafaka a Hong Kong ba sa samun damar yin aiki a yankin, ko da sun shafe shekaru da zama a garin.

Wasu daga cikin' yan wasan na atiseyeHakkin mallakar hotoALL BLACK FC
Image captionAkasarin ‘yan wasan basa iya aiki ta hallaltaciyyar hanya a Hong Kong

A cikin shekaru biyar da suka gabata ne Darius, mai neman mafaka daga Togo, ya iso Hong Kong .

Shi ne kyaftin din ‘yan wasan kwallon kafar, kuma ya ce wasan kwallon kafa na karfafa masa gwiwa, saboda an hanasu neman aiki a yankin.

“Akwai wahala. Yana sa mutane su ji kamar sun shiga tsaka mai wuya saboda ka yi shekara biyar zuwa bakwai kana zaman jira. Za ka soma tunanin yadda makomarka zata kasance.” In ji Darius?

Sai dai ya samu kwarin gwiwa bayan da ya shiga cikin kungiyar kwallon kafa.

Ga yan wasan da suka nuna bajinta sosai kuwa wasan na bude musu kofofin samun nasara a rayuwa. Wasu kalilan daga cikinsu na samun damar zuwa kananan kungiyoyin kwallon kafa, kuma daga nan za su iya neman bizar yin aikin ta hallataciyyar hanya a yanki Hong Kong.

KyaftinDarius (tsakiya) da Medard wanda ya kfa kungiya (dama ) sun zauna kusa 'yan wasa biyuHakkin mallakar hotoALL BLACK FC
Image captionKyfatin Darius (tsakiya) da kuma Medard wanda ya kafa kungiya (dama ) na son su zama wadanda za su rika marawa ‘yan wasan baya

Jama’a na daukar hoto tare da rufe hancinsu

Darius ya kuma ce abu ne mai wuya masu gida su ba bada hayar gidajensu ga bakin haure, saboda da dama daga cikinsu basa son ‘yan kasashen waje.

Solomon Nyassi, mai shekara a 26 daga kasar Gambiy ya shaidawa BBC cewa wasu mutane sun toshe hancinsu idan sun zo wuce shi a kan titi a Hong Kong.

Ya kuma ce a wasu lokutan idan yana tafiya kan titi, wasu sinawa masu yaon bude ido na tambayarsa ko za su iya daukar hoto da shi? kuma wannan kansa ya ji kunya”.

A karawar da kungiyar All black FC ta yi da wata kungiyar kwallon kafa ce Solomon ya hadu da buduwarsa ,Louise Chan mai shekara 20, yar yankin Hong Kong ce.

Ta ce mazajen Afrika sun fi sanin ya kamata kuma iyalinta sun amince da saurayinta.

Sai dai ta ce yadda wasu suke magana idan sun gansu yana ba ta mamaki .

“Yan Hong Kong mutane ne da basu san ya kamata ba,” a cewar Louise, wadda take da shagon sayar da tufafi . “Akwai sakwannin da aka turo min da ke yada jita-jita kan ‘yan Afrika, Kuma ban ji dadin hakan ba.”

Dan wasa Solomon d budurwarsa Louise sun dauki hoton selfie sun murmushiHakkin mallakar hotoLOUISE CHAN
Image captionSolomon da budurwasa Louise sun fuskanci tsangwamma daga wurin wasu mutane
Presentational white space

Sai dai ana samun masu nuna wariyar launin fata a filin wasa.

Darius ya ce wasu yan Hong Kong na ganin ‘yan AfriKa na keta idan suna wasan kwallon kafa. Wasu daga cikin cikinsu kan yi mu su ihu .

“A ko yaushe muna fadawa ‘yan wasannmu su kasance ma su ladabi da biyayya,” a cewar kyaftin.

 Ban taba nuna wariyar launin fata ba 

Doug Tze, mai shekara 34 dan yankin Hong Kong ne, kuma tun daga shekarar 2017 ya ke wasa a kungiyar All Black FC .

Ya ce da farko ya ji kamar ba a so zuwansa ba, kuma ya dora alhaki a kan yadda yan yankin su ka rika mu’amumala da ‘yan Afrika.

Sai dai bai karaya ba kuma a yanzu sun zama abokai da wasu daga cikin ‘yan wasan.

All Black FC na karawa da Biu Chun Rangers, wadanda suke wasa a gasar Primiya ta the Hong KongHakkin mallakar hotoBIU CHUN RANGERS
Image captionAll Black FC na karawa da Biu Chun Rangers, wadanda suke wasa a gasar Primiya ta the Hong Kong

Kevin Fung, wanda dan wasan kwallon kafa ne a wata kwaleji wanda a baya ya taka leda a kungiyar All Black FC ya yi ammanar cewa ‘yan Afrika za su iya karfafa gwiwar ‘yan Hong Kong.

“Suna da juriya kuma suna da kwazo. Amma ‘yan wasan Hong kong sun cika karaya da wuri,” in ji Kevin.

“Yan Hong Kong sun fi maida hanaklin kan kartu da aiki. Lokaci kalilain suke da shi ga wasan kwallon kafa.

Game da haka ana nuna shakku a kan tasrin wasan kallon kafa wajan shawo kan matslar wariyar launin fata a Hong Kong.

“Wasan kwallon kafa na cikin gida ba shi da kwarjini sosai,” in ji Kevin. Ya ce . “Wasanni kalilan ne ake nunawa a kafofin watsa labarai, babu wanda ya damu da wasan kwallon kafa. Shawo kan matsalar wariyar launin fata zai kasance wani abu mai wahala.”

Sai dai ‘yan wasan All Black FC sun fahimci wannan. Kuma domin su cimma burinsu na sauya tunanin alumma, ‘yan wasan a wasu lokutan kan ziyarci gidan kula da tsoffafi domin su yi aiki kyauta.

“Watakila ba mu ne za mu ci moriyar wannan aiki a yanzu ba, amma zai taimakawa wadanda za su zo nan gaba ta yadda za a rika ganin kimar kabilu marasa rinye da masu neman mafaka da kuma ‘yan gudun hijira .”in ji Darius.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *