Zaben 2019: Me Buhari ya gaya wa Tinubu a Landan?

buhariHakkin mallakar hotoBASHIR AHMED TWITTER
Image captionBola Tinubu bai halarci manyan tarukan da jam’iyyar ta yi ba na baya-bayan nan

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa ta musamman da jagoran jam’iyyarsu ta APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a birnin Landan.

Mai taimakawa shugaban na musamman kan kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmad ne ya wallafa batun ganawar tasu a shafinsa na Twitter.

Sai dai bai yi wani karin haske kan dalilin ganawar tasu ba, wacce aka yi ranar Lahadi da daddare.

Amma wasu na hasashen cewa ganawar ba za ta rasa nasaba da zaben 2019 ba da kuma aniyar da shugaban ya bayyana ta neman tazarce.

Har ila yau ana ganin shugaban zai yi yunkurin shawo kan dattijon jam’iyyar kan wasu batutuwa da ake ganin ba ya jin dadin yadda suke gudana, musamman wadanda suka shafi batun shugabancinta.

Hakazalika akwai yunkurin dinke barakar da ke kunno kai a jam’iyyar APC ba a jihohi daban-daban na kasar, gabannin babban taron APC din, wanda Tinubu ke jagoranta.

Rashin jituwa na sake tasowa a jam’iyyar a daidai lokacin da babban zaben kasar ke kara karatowa.

A watan Fabrairu ne shugaban Buhari ya sanya Tinubu, a matsayin mutumin da zai jagoranci yunkurin da ake yi na dinke barakar da ke jam’iyyar APC.

Wasu masana harkokin siyasa suna kallon batun a wani gagarumin aiki da ba a taba yi ba a kasar ta fuskar rikicin siyasar cikin gida.

Buhari da TinubuHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionShugaba Buhari ya zabi Tinubu don sasanta rikicin jam’iyyar APC a jihohi

A ranar Lahadin ne dai kuma APC ta fitar da jerin sunayen wadanda za su shirya babban taron jam’iyyar, karkashin jagorancin Gwamna Badaru Abubakar na jihar Jigawa.

A ranar 8 ga watan Afrilu ne Shugaba Buhari ya tafi Birtaniya don fara wata ziyarar aiki, inda ake sa ran zai gana da Frayi Ministar kasar Theresa May da shugannnin wasu kamfanonin hakar mai.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *