Trump ya gayyaci Buhari zuwa Amurka

BuhariHakkin mallakar hotoFACEBOOK PRESIDENCY
Image captionBabu tabbas ko Shugaba Buhari zai kalaubalanci Trump kan kalaman da ake ce ya yi na batanci kan kasashen Afirka

Shugaba Amurka Donald Trump, zai gana da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadar White House karshen watan Afrilu.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta Amurka ta fitar ta ce, shugabannin za su tattauna ne a kan yadda za a bunkasa tattalin arziki da yaki da ta’addanci da kuma yadda Najeriya za ta zama jagora a bangaren mulkin dimokradiyya a nahiyar yammacin Afirka.

A cikin watan Janairun da ya wuce, Shugaba Trump ya bayyana cewa ‘Kasashen Afirka wulakantattu ne’, kalaman daga bisani Mista Trump ya musanta.

Sai dai kawo yanzu babu tabbas a kan ko Shugaba Buhari zai amsa gayyatar Mr Trump.

A shekarar 2015, tsohon Shugaban Amurka Barack Obama ya taba gayyatar Buhari fadar White House.

Wannan layi ne

Karin bayani

A kwanakin baya, shugaban Amurkan, ya kori sakataren harkokin wajensa Rex Tillerson daga kan mukaminsa a lokacin yana ziyara a Najeriya, inda har ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari, ya kuma jaddada aniyyar kasarsa wurin taimakawa Najeriyar kan yaki da ta’addanci.

Sannan Mr Tillerson din ya kuma yi alkawarin cewa Amurkan za ta taimaka wajen ceto ragowar ‘yan matan sakandaren Chibok da Boko Haram ta sace su 112, alkawarin da Shugaba Buhari ke son Mr Trump ya cika.

Akwai alaka mai karfi tsakanin Amurka da Najeriya kan tattalin arziki da kuma siyasa.

Ba ya ga haka kasashen biyu na aiki tare a wurin yaki da ta’addanci a yankin Afirka ta Yamma.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *