Takarar Buhari : PDP ce ta firgita shi da APC – Sule Lamido

Sule LamidoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionSule Lamido ya ce wadanda suka mara wa Buhari baya ya ci zabe ‘yan PDP ne kuma yanzu sun bar APC sun koma PDP za su ga yadda zai sake cin zaben

Tsohon gwamnman jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce taron da PDP ta yi a jihohin Jigawa da Katsina ne ya firgita APC har shugabannin jam’iyyar suka roki Shugaba Muhammadu Buhari ya fito ya ayyana cewa zai sake yin takara.

A wata hira da ya yi da BBC Sule Lamido ya ce : ”Ai taron da aka yi a Jigawa da na Katsina shi ya firgita su, suka ce ranka ya dade gara fa ka zo, domin yadda aka yi taron nan na Jigawa da Katsina, idan ba ka zo ka ce za ka yi takara ba mun shiga uku…”

Tsohon gwamnan ya kara da cewa APC da Buharin sun yi hakan ne domin su samu dan hutu na ”Tsunamin” da PDP ta yi a jihohin biyu a tarukanta.

Ya ce sai ma jam’iyyar tasu ta yi irin taron a Sokoto da Kaduna da Kebbi kafin kuma ta yi na Abuja lokacin da hankalin shugaban da jam’iyyarsa za su fi tashi.

Tsohon ministan harkokin wajen ya ce ba su da wata fargaba kan ayyanawar da Shugaban ya yi cewa zai sake yin takara, domin ai ‘yan PDP ne suka haife APC, saboda haka Buhari jikansu ne, kuma ”don zai yi takara mene ne abin damuwa?”

Sule Lamido ya ce tun da Buhari yake tsayawa takara sau uku ko hudu bai taba cin zabe ba sai da gwamnonin PDP biyar da wasu jiga-jiganta irin su Atiku da Wamakko da Goje da Abdullahi Adamu da Kwankwaso da Bukola da sauransu suka mara masa baya.

Kuma ya ce ko da ma Buharin zai sake takara ai wadanda suka mara masa baya ya ci zabe a yanzu sun bar APC sun koma gidansu PDP, don haka ba su da wata fargaba a kan takararsa, domin daman shi a karan-kansa bai taba cin zabe ba.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *