Za a mayar da maboyar Ojukwu gidan tarihi

OjukwuHakkin mallakar hotoAFP
Image captionLaftanal Kanar Chukwuemeka Ojukwu ya rasu a ranar 1 ga watan Maris na shekarar 2012

Mahukunta a jihar Anambra da ke kudancin Najeriya sun ce za a ma ida wata maboyar karkashin kasa da tsohon madugun ‘yan aware na Biafra ya rika amfani da ita a lokacin yakin basasar kasar ta zama gidan tarihi.

A shekarun 1960 ne Laftanal Kanar Chukwuemeka Ojukwu ya jagoranci yakin basasar wanda ya jefa kasar cikin tashin hankalin da ba ta taba ganin irinsa ba.

Akwai kuma wadansu koguna da wani wurin da ruwa ke kwarara daga saman dutse da su ma za a mayar da su wuraren shakatawa domin masu yawon bude ido.

Mai magana da yawun da gwamnan jihar, Willie Obiano, ya ce: “Wadannan wuraren yawon bude idanu za a ba su muhimmanci sosai ta hanyar gina hanyoyin da za su rinka kai mutane wajen”.

Ana kallon wannan yunkuri a matsayin hanyar samar da aikin yi da kuma samar da kudin shiga ga yankin.

  • ‘Yan Biafra na son kifar da gwamnatin Buhari’
  • Kun san mutumin da ke son a raba Nigeria?

Ojukwu, ya ayyana kafa kasar Biafra a shekarar 1967, lamarin da ya janyo yakin basasa inda mutum fiye da miliyan daya suka rasa rayukansu galibinsu saboda yunwa da kuma cututtuka.

Marigayi Ojukwu yana daya daga cikin mutanen da ake tunawa da su wadanda suka yi fice a kudu maso gabashin Najeriya.

Wannan layi ne

Kun san yadda Biafra ta samo asali?

Chukwuemeka OjukwuHakkin mallakar hotoAFP
Image captionJagoran ‘yan awaren ya yi gudun hijira zuwa kasar Ivory Coast kafin a yi masa afuwa daga baya

Biafra wata kalma ce da masu fafutikar ballewa daga Najeriya a yankin Kudu maso Gabashin kasar suke amfani da ita wajen bayyana fatansu na ganin sun kafa kasar kansu – wadda su kai wa lakabi da “Jamhuriyar Biafra”.

Sunan Biafra ya samo asali ne da gabar mashigin tekun Atlantic da ke yankin Kudu maso Gabashin kasar.

Galibi mutanen da suke zaune a yankin ‘yan kabilar Igbo ne amma akwai wasu kabilu kamar Efik da Ibibio da Annang da Ejagham da Eket da Ibeno da kuma Ijaw.

Kokarin ballewar yankin daga Najeriya shi ne babban dalilin da ya jawo yakin basasar kasar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum miliyan biyu galibi saboda yunwa.

A shekarar 1960 ne Najeriya ta samu ‘yancin kai daga Birtaniya. Galibin jama’ar da ke yankin arewacin kasar Musulmi ne, yayin da mafi yawan Kiristoci suke zaune a kudanci.

A lokacin Najeriya ta kunshi shiyyoyi uku ne wato arewa (wadda Hausawa suke) da kudu maso yamma (yankin kabilar Yarabawa) da kuma kudu masoi gabas (na kabilar Igbo).

An samu sauyin gwamnati a kasar, bayan juyin mulkin watan Janairun 1966 inda aka kashe Farai Ministan farko Sir Abubakar Tafawa Balewa da Firimiyan Jihar Arewa Sir Ahmadu Bello da kuma sauran manyan jagororin arewa da na Yarabawa.

Jana’izar ban girma

Ana yi wa juyin mulkin kallon wanda ‘yan kabilar Igbo suka kitsa saboda yadda ba a kashe shugaban kasa na lokacin ba wato Nnamdi Azikiwe, wanda Igbo ne.

Daga nan ne sai Janar Aguiyi Ironsi ya zama shugaban mulki soji na farko a Najeriya.

Sai dai a watan Yulin shekarar 1966 wasu sojoji daga arewa suka kifar da gwamnatin Ironsi, inda Janar Yakubu Gowon wanda ya fito daga arewa ya zama shugaban mulkin sojan Najeriya.

OjukwuHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionGawar marigayi Ojukwu lokacin da aka yi masa jana’izar ban girma a shekarar 2012

Juyin mulkin biyu sun kara ruruta wutar kabilanci a kasar.

An rika samun kashe-kashen kabilanci a arewa, inda ake kashe ‘yan kabilar Igbo hakazalika an kashe ‘yan arewa a matsayin ramuwa a wasu biranen gabashin kasar.

An yi tarurruka tsakanin manyan sojoji da jami’an ‘yan sandan kowane yanki da fatan ganin an warware matsalar cikin ruwan sanyi. Sai dai hakan bai yiwu ba.

A ranar 30 watan Mayun 1967 ne Gwamnan Soji na Yankin Gabashin Najeriya Laftanal Kanar Chukwuemeka Ojukwu ya ayyana yankin gabashin kasar a matsayin kasa mai cin gashin kanta wadda ta balle daga Najeriya kuma ya sanya mata suna “Jamhuriyar Biafra”.

Wata 30 aka kwashe ana yakin basasar wato daga ranar 6 ga watan Yulin 1967 zuwa ranar 15 ga watan Janairun 1970, inda Kanar Ojukwu ya ce ya mika wuya ga dakarun Najeriya.

Jagoran ‘yan awaren ya yi gudun hijira zuwa kasar Ivory Coast, inda ya kwashe lokaci mai tsawo a can kafin gwamnatin Shehu Shagari ta yi masa afuwa.

Ojukwu ya rasu a ranar 1 ga watan Maris na shekarar 2012.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *