Manchester United 2-0 Brighton & Hove Albion

Yadda aka fafata: Manchester United 2-0 Brighton

Romelu Lukaku ya ci kwallonsa ta 12 a gasar FA yayin da man U ta doke Brighton kuma kungiyar ta kai matakin dab da na karshe kenan.

Lukaku ya ci kwallo ta farko ne da ka bayan da Nemanja Matic ya aika masa da wani kuros, kuma shi ne ya ci kwallo ta biyu daga wani firikik daga Ashley Young.

Wanna na nufin cewa Manchester United na da damar cin wata gasa a kakar wasan bana bayan da Sevilla ta yi waje da ita daga gasar Zakarun Turai.

Kawo yanzu, babu kungiyar da ta saka wa United kwallo a raga a gasar ta FA a bana.

Brighton ta rika kai farmaki sau da yawa kafin a karshe Matic ya kwaci kungiyarsa.

Romelu LukakuHakkin mallakar hotoREUTERS
Image captionRomelu Lukaku ya ci kwallo 25 a wasanni 44 da ya buga wa Manchester United a karkar wasa ta bana.
BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *