Shin ‘yan majalisa na shirin yi wa Buhari wayo a zaben 2019 ne?

Majalisun dokokin tarayyar Najeriya sun ce sun sauya fasalin tsarin zaben 2019 ne domin Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya samu damar sanya ido a zabukan.

A gyaran da ‘yan majalisun suka yi wa tsarin zaben, za a soma ne da zaben majalisar dokokin tarayya kuma zaben shugaban kasa ne zai zo a karshe.

  • ‘Buhari ne ya jefa Nigeria a yunwa da talauci’
  • Me ‘yan Nigeria ke cewa kan wasikar Obasanjo ga Buhari?

Wasu ‘yan kasar sun soke su kan hakan, suna masu cewa matakin tamkar wata dama ce ga ‘yan majalisar su lashe nasu zaben sannan su yi watsi da shugaban kasa.

Sai dai dan majalisa Mohammed Musa Soba ya shaida wa BBC cewa “mun dauki matakin ne domin mu bai wa shugaban kasa damar sanya ido kan zabukan da za su zo kafin nasa.”

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *