Tinubu ne zai jagoranci sasanta ‘yan APC — Buhari

Bola TinubuHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionBola Tinubu na cikin wadanda suka mara wa Buhari baya a zaben 2015

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada tsohon gwamnan jihar Legas Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin mutumin da zai jagoranci yunkurin da ake yi na dinke barakar da ke jam’iyyar APC mai mulkin kasar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar ta ce Bola Tinubu “zai shugabanci kokarin ganawa da sasanta da kuma inganta zaman da ake yi a All Progressives Congress(APC).”A cewar sanarwar, wasu daga cikin abubuwan da ake sa ran jigon jam’iyyar ta APC ya aiwatar sun hada da dinke barakar da ke tsakanin mambobi da shugabanni da masu rike da mukaman jam’iyyar a jihohi da kuma kasa baki daya.

  • El-Rufai da Saraki ne suka hana ni zama mataimakin Buhari —Tinubu
  • Me ya sa APC ta kasa zama dunƙulalliyar jam’iyya?

Jam’iyyar ta APC dai ta fada cikin rigingimun cikin gida tun bayan da ta lashe zaben shekarar 2015.

Wadanda suka fi fitowa fili su ne rigimar da ake yi tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso da mutumin da ya gaje shi, Abdullahi Umar Ganduje da wanda ake yi tsakanin gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da bangaren sanata Shehu Sani.Ana sa ran kwamitin da Bola Tinubu zai jagoranta zai yi sulhu a rikicin jam’iyyar APC da ke faruwa a Zamfara, Oyo, Kogi da dai sauransu.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *