Iran ta yi barazanar yin raddi ga Amurka

Amurka ta caccaki Iran kan murkushe masu zanga-zangaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionAmurka ta caccaki Iran kan murkushe masu zanga-zanga

Iran ta ce Amurka ta “wuce gona da iri” saboda takunkumin da ta sanya wa shugaban bangaren shair’a na kasar, Ayatollah Sadeq Amoli-Larijani.

Ma’aikatar wajen kasar ta sha alwashin mayar da martani, ko da yake ba ta fadi irin matakin da za ta dauka ba.

Kazalika Iran ta yi watsi da duk wani yunkuri na sauya sharudan da kasashen Yamma suka gindaya mata kan shirinta na kera makami mai linzami.

Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya sha sukar yarjejeniyar da aka kulla da Iran a 2015, ya fada ranar Juma’a cewa zai tsawaita sassaucin takunkunkumin da aka kakaba wa kasar a karon karshe.

A lokaci guda kuma, Amurka ta sanya sabon takunkumi kan kamfanoni da mutane 14 na kasar ta Iran saboda zargin yin amfani da mukamai ba bisa ka’ida ba.

Shugaba Trump ya ce yana bai wa Turai da Amurka dama ta karshe domin su magance abin da ya kira “kura-kuran” da suka yi wajen kulla yarjejeniya da Iran a shekarar 2015.

Fadar White House na so kasashen Turai da suka sanya hannu kan yarjejeniyar su amince a haramtawa Iran kera makamai masu linzami har abada.

A yarjejeniyar da aka amince da ita, haramcin zai kare ne a shekarar 2025.

Kazalika Mr Trump yana so a dauki mataki kan shirin Iran din na kera makamai masu linzamin da ke cin dogon zango.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *