Ta-zarce ba za ta hana ni korar malamai ba – El-rufai

El-RufaiHakkin mallakar hotoFACEBOOK/KADUNA STATE GOVERMENT

Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufai ya ce babu wata zanga- zanga da za ta shi sauya matakin da ya dauka na korar ma’aikata fiye da dubu 30 a jihar.

Gwamnan dai na mayar da martani ne ga wata zanga- zanga da malaman makaranta da kuma ma’aikatan kananan hukumomi suka yi a wannan makon don nuna adawa da wannan matakin.

Ya bayyana hakan ne jiya Juma’a a wata zantawa da manema labarai a Abuja.

Hakazalika ya ce yana sauye-sauye a fannin ilimin jihar domin kawo gyara.

“Ni makarantar gwamnati na yi. Abin da nake so shi ne irin ingantaccen ilimin da na samu suma ‘ya’yan talakawa su samu,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: “ta yadda su ma ‘ya’yan talakawa Allah zai daukaka su kamar yadda zai daukaka ‘ya’yan masu hannu da shuni.”

  • Za a sallami malamai fiye da 20,000 a Kaduna
  • Kalli zanga-zangar ma’aikata a Kaduna
  • Buhari ya goyi bayan sallamar malamai 22,000

Daga nan ya ce abin da suka sa a gaba ke nan kuma “ba za su sauya ba.”

Har ila yau, gwamnan ya ce sun dauki matakan daukar malamai dubu 25 wadanda su ne za su cike guraben wadanda aka kora.

Ya kuma kara jaddada cewa “magana ko zanga-zanga ba zai canja” wannan matakin da suka dauka ba.

Hakazalika gwamnan ya kare matakin gwamnatinsa na korar ma’aikatan kananan hukumomi wadanda ya ce “sun yi yawa kuma yawancinsu ba su zuwa wurin aiki.”

Ya ce kudin da ake kashe musu za a yi amfani da su ne wajen yi wa al’umma aiki.

A karshe ya ce hankalinsa ba ya tashi kan ko watakila matakan da yake dauka za su iya shafar damarsa ta kara cin zabe a jihar nan gaba.

“Allah shi ke ba da mulki, shi ke kwacewa. Zabe… mutane na yin abin da Allah Ya kaddara za su yi ne. Mu zuciyarmu fara ce,” in ji shi.

Ya kara da cewa: “Talaka muke son mu kare mutuncin shi da mutuncin ‘ya’yansa kuma Allah Ya san haka. Saboda haka mun dogara ga Allah.”

“Idan Ya ga mun cancanta a ba mu mulkin nan Ya ba mu, idan kuma ya ce gara a ba wanda zai daga martabar jihar Kaduna wallahi ba mu da wata matsala. Allah Ya yi mana zabin alheri,” in ji el-Rufai.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *