Abin da Zakzaky ya fada wa ‘yan jarida

A watan Disambar 2015 aka kama El-ZakzakyHakkin mallakar hotoPR NIGERIA
Image captionA watan Disambar 2015 aka kama El-Zakzaky

Shugaban kungiyar ‘Yan Uwa Muslumi da aka fi sani da ‘yan Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya gana da manema labarai karon farko tun bayan da aka kama shi.

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ce ta kama Sheikh El-Zakzaky a watan Disambar shekarar 2015 a Zaria da ke jihar Kaduna, bayan sojoji sun yi wa gidansa kawanya.

  • Jonathan ya soki Buhari kan Zakzaky
  • Kotu ta umarci gwamnati ta saki El-zakzaky

Wata sanarwa da kafar watsa labarai ta PR Nigeria fitar na dauke da hotunan Malamin a lokacin da yake jawabi ga ‘yan jaridar.

Gidan talbijin na Channels ya ambato Sheikh El-Zakzaky na cewa yana nan a raye kuma lafiyarsa lau.

Ya kuma gode wa ‘yan Najeriya saboda addu’o’in da suke yi masa.

A makon nan ne dai aka yi jitar-jitar cewa Malamin ya rasu.

Ga yadda ganawarsa ta kasance da ‘yan jarida:

‘Yan jarida: Barka da rana?

Sheikh Zakzaky: Wane hali kake ciki?

‘Yan jarida: Ko za ka iya ganawa da mu?

Sheikh El-Zakzaky: Idan sun abinci kuma sun ba ni izini (kamar yadda ya ce cikin raha)

‘Yan jarida: Yaya kake ji yanzu haka?

Sheik El-Zakzaky: Ina samun sauki jami’an tsaro sun bari na gana da likitan. Ina godiya ga Allah. Ina samun sauki.

‘Yan jarida: Kana da wani abu da za ka kara cewa.

Sheikh El-Zakzaky: Ina godiya ga addu’o’inku.

‘Yan jarida: Mun gode

Sheikh El-Zakzaky: Na gode.

El-ZakzakyHakkin mallakar hotoPR NIGERIA
Image captionEl-Zakzaky

Umarnin kotu

Sau da dama kotunan kasar suna bayar da umarni ga gwamnatin Najeriya ta saki Malamin, sai dai ba ta yi hakan ba.

Mabiya Malamin sun gudanar da jerin zanga-zanga da zummar matsa lamba ga gwamnatin ta sake shi.

Sun yi zargin cewa ana tsare da shi ba bisa ka’ida ba, ko da yake ministan shari’ar kasar Abubakar Malami ya shaida wa BBC kwanakin baya cewa suna ci gaba da tsare shi ne saboda sun daukaka kara a kan umarnin da kotunan suka bayar.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *