Mutumin da ya samar da hanya domin yara su rika ziyartar kauyensu

Jalandhar Nayak
Image caption“Bukata ta ita ce in samar da hanya,” inji Mista Nayak mai shekar 45 da haihuwa.

Wani mutum a jihar Orissa ta kasar India ya gina wata hanya mai tsawon kilomita 8 da diga saboda ‘ya’yansa masu zuwa makaranta su sami sukunin ziyartarsa a-kai-a-kai.

Jalandhar Nayak mai shekara 45 na zaune ne a wani kauye mai nisa, kuma yana da nisan misalin kilomita 10 daga makarantar da ‘ya’yansa uku ke karatu.

Amma ‘ya’yan nasa na shafe awa uku kullum kafin su kai makarantar, domin sai sun hau wasu manyan duwatsu guda biyar.

Mutumin ya shafe shekaru biyun da suka wuce yana yin hanyar, kuma ya kan bata awa takwas na kowane yini yana saran dutse da cire duwatsu.

  • Budurwa ta kashe kanta don an hana ta soyayya da Musulmi a India
  • Za a daure namijin da ya yi saki uku a take a India

Ya fada wa manema labarai na yankin cewa yana fatan ‘ya’yan nasa zasu sami sukunin ziyartarsa a kowane karshen mako da lokutan hutu da zarar ya kammala aikin hanyar.

Gwamnatin yankin ta ce zata karasa sauran aikin hanyar, kuma ta yi alkawarin biyan Mista Nayak kudin aikin da ya riga ya yi.

Kafofin watsa labarai suna kwatanta Mista Nayak da Dasharath Manjhi wanda aka fi sani da sunan “mutumin dutse” na jihar Bihar wanda shi kadai ya haka manyan duwatsu domin samar da wata hanya da ta hada kauyensu da wani gari da yake makwabtaka da kauyen.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *