Ali Bongo zai zama shugaban ‘mutu ka raba’ a Gabon

Gabon Ali BongoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionShugaba Ali Bongo ne ya rage ya sanya hannu kan sabon kundin tsarin mulkin

Majalisar Gabon ta amince da sabon kudin tsarin mulki da zai ba shugaban kasar Ali Bongo damar ci gaba da mulki har abada.

Sabon kudin tsarin mulkin mai cike da sabbin dokoki ya samu amincewar ‘yan majalisar wakilai da dattijai da gagarumin rinjaye.

Sai dai ‘yan adawa a kasar sun ce wannan ya nuna ana neman mayar da Gabon tsarin mulkin sarauta.

A baya can, Gabon na bin tsarin wa’adi biyu na shekaru bakwai ga shugaban kasa amma a sabon kudin tsarin mulkin, babu iyaka ga wa’adin shugaban kasa.

Hakan na nufin Shugaba Ali Bongo na iya ci gaba da mulki a Gabon har mutuwa.

  • Gabon: An kama ‘yan adawa 1000
  • EU: An yi magudi a zaben Gabon

Kuma sabon kudin tsarin mulkin ya kara masa karfin iko fiye da majalisa.

Sannan sabon kudin ya ba shugaban kasar rigar kariya, ko bayan ya sauka daga mulki.

Yanzu shugaba Ali Bongo ne ya rage ya sanya hannu kan sabon kundin tsarin mulkin nan da kwanaki 15.

Gabon Ali BongoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMagoya bayan shugaban adawa Jean Ping sun yi watsi da sakamakon zaben 2016.

Sau da dama dai a bunkasar mulkin dimokuradiya a kasashen Afirka ana kayyade wa’adin shugaban kasa.

Amma kusan rabin gwamnatocin yankin sun yi kokarin canza tsarin, lamarin da ya haifar da jerin zanga-zangar adawa da gwamnatocin kasashen Burkina Faso da Burundi da Jamhuriyyar dimokuradiyar Congo da kuma Congo Brazzaville.

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kamfanin Afrobarometer ya gudanar, sakamakon ya nuna cewa yawancin mutanen kasashen Afirka 34 suna goyon bayan takaita wa’adin shugaban kasa zuwa wa’adi biyu.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *