‘Yan Kamaru na tserewa zuwa Nigeria

KamaruHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Image captionYankin da ke magana da Ingilishi na neman ballewa daga Kamaru

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane 15,000 ne suka tsallako Najeriya daga Kamaru tun a watan Nuwamba sakamakon rikicin masu neman ballewa daga kasar.

Tun a bara ne rikici ya barke a yankin da ke magana da harshen ingilishi da ke zanga-zangar neman ballewa daga Kamaru.

Hukumomin Najeriya da Majalisar Dinkin Duniya sun ce kusan a kullum ne mutane ke ficewa daga Kamaru zuwa garuruwan Najeriya da ke kan iyaka da Kamaru.

Yawancinsu ‘yan gudun hijirar mata ne da yara kanana da ke magana da harshen ingilishi.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana tattaunawa da hukumomin Najeriya domin tanadin sansani ga ‘yan gudun hijirar.

Hukumar ta ce ta yi rijistar mutane 15,000, kuma akwai wasunsu da dama da ke jira.

  • Wa ya kama shugaban ‘yan a-waren Cameroon a Nigeria?
  • Gudun hijira: Nigeria da Kamaru sun kulla sabuwar yarjejeniya

Mutanen dai na tserewa ne saboda gujewa kamen mutane da ake yi kan zanga-zangar adawa gwamnatin Kamaru da aka shafe watanni ana yi a yankin da ke magana da harshen ingilishi.

A makon da ya gabata ne, rahotanni suka ce hukumomin tsaron Najeriya da ke aiki tare da takwarorinsu na Kamaru suka cafke Julius Ayuk Tabe shugaban ‘yan a waren na Kamaru a birnin Abuja na Najeriya.

Julius Ayuk Tabe shi ne shugaban kungiyar da ke neman ‘yancin yankin Ambazonia.

Kuma an kama shi ne tare da wasu mutane shida a lokacin da suke fara wani taro kan ‘yan gudun hijirar da suka tsere zuwa Najeriya daga kudancin Kamaru domin tashe-tashen hankulan da ake fama da su a yankin.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi gargadin cewa za a sami karin dubban ‘yan gudun hijira da za su shigo Najeriya daga Kamaru idan har rikicin ya ci gaba.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *