Mece ce Tashar ruwa ta kan tudu?

Inland dry portHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionTashar ruwa ta kan tudu

Shugaba Muhammadu Buhari ya bude wata tashar ruwa ta kan tudu ta farko a Najeriya, kuma a birnin Kaduna dake arewa maso yammacin kasar.

Wannan tasha za ta taimaka wa ‘yan kasuwar yankin arewacin kasar wajen rage wahalhalun zuwa kudancin kasar domin karbar kayansu ko fitar da su daga Najeriya ba tare da kashe kudaden fito da na sufuri ba.

Mecece tashar ruwa ta kan tudu?

Amma akwai wasu tashoshin da akan gina a wasu wurare dake nesa da tashar jirgin ruwa da ake kira tashar ruwa ta kan tudu.

Ita wannan tashar ta na iya kasancewa mai nisan daruruwan kilomita daga gabara teku, kuma akan hada tashar gabar teku da wannan tashar ta kan tudu da titunan mota ko hanyar jirgin kasa.

Kuma tashar wata cibiya ce ta hada-hadar kayan da ake shigar su cikin kasar.

  • An dakatar da masu tukin jirgin saman da suka yi fada a cikin jirgi
  • An ceto mutum 19 a hatsarin jirgin ruwa a Legas
Inland dry port
Image captionTashar na taimakawa wajen samar da wuraren ajiyar kaya daga jiragen ruwa cikin hanzari

Bayan wannan aikin, tashar ruwa ta kan tudu na samar da wasu muhimman wurare na ajiyar kaya da kula da na’urorin sufuri da ayyukan kwastan.

Sannan akan tsara wurin da ake gina tashar ruwa ta kan tudu domin ta kawo saukin cunkoson da ake fama daga ita tashar jirgin ruwa dake kasar.

Kana tashar na taimakawa matuka wajen sauke kaya daga jiragen ruwa cikin hanzari, kuma ta kan inganta yanayin sufurin kasar.

Inland dry port
Image captionWasu madaukin kaya wato kontena a tashar ruwa ta kan tudu ta Kaduna

Tashar gabar teku ko ta kan tudu?

Akwai rudani dangane da banbancin tashar ruwa ta kan tudu da tashar madaukin kaya, wato kontena.

Akan aje tashar madaukin kaya, ko kontena ne domin su a yankunan kasa, kuma bayan an sauke kaya daga cikin kontenar, akan dawo da su wannan cibiyar domin’yan kasuwa su yi amfani da ita wajen saka kayan da suke bukatar fitarwa daga wannan kasar.

Amma tashar ruwa ta tudu kuwa wata tsararrar cibiya ce ta da aka gina domin ta tallafa wa tashar jirgin ruwan kasar ta hanyar samar da dukkan ayyukan da ake yi a tashar gabar tekun a wani wuri dake cikin kasar.

In the case of the proposed Inland Port, somewhere in central Saskatchewan, the task will be to reduce both congestion in the coastal ports and also dwell time of ships in port.

Tashar da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya kaddamar a yau a Kaduna tashar ruwa ta kan tudu ce.

Zata samar da dukkan ayyukan da ake yi a babbar tashar jirgin ruwa dake birnin Legas.

A takaice, wannan tashar zata kawo gagarumin sauki ga tashoshin jirginruwan Najeriya, domin da zarar kayan arewacin Najeriya sun isa babbar tashar jirgin ruwa ta gabar teku, sai kawai a wuce da kayan zuwa waccan tashar ta kan tudu kai tsaye, inda masu kayan zasu nufa domin karabar kayan nasu.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *